Labarai

Datti Assalafy yayi Martani mai zafi kan Maganganu Buhari Hirarsa da Yan jarida

Hirar da ankayi da Muhammadu Buhari a karkashin gidan talabijin din tambarin hausa tv wanda a jiya me sunka saki cikakkiyar hirar da su kayi da Muhammadu Buhari a gidan Gwamnatin tarayya inda wannan hirar ta tayar da kura sosai irin yadda buhari yake fadin maganganu wanda wasu yan gani kashenin Buhari suke ganin baida masaniya akan wadannan abubuwa. Daya daga cikin masoyansa kuma marubuci a kafar sada zumunta Datti Assalafy ne yayi wannan tsokaci wanda ya baiwa mutane mamaki sosai.

Datti Assalafy yayi Martani mai zafi kan Maganganu Buhari Hirarsa da Yan jarida
Datti Assalafy yayi Martani mai zafi kan Maganganu Buhari Hirarsa da Yan jarida

“ABIN KUKA ABIN TAKAICIA she Maigirma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da saninsa ya azabtar damu da yunwa?

Anya kuwa wannan Baba Buharin mu Maigaskiya ne da muka zaba har yake mana gatse da horon yunwar ciki?

Anya kuwa maciya amana basu canza mana shi ba kuwa?

Hakane talaka yaje yayi noma, to ina kudin taki? buhun taki daga dubu 3 ya kuma dubu 23 ta ina talaka zai iya noma ba’a bashi subsidy na taki ba?

Da na saurari wanna cikakken hira da akayi da Baba Buhari Maigaskiya sai da na kusan zubar da hawaye saboda takaici da bakin ciki

Dattijo Baba Buhari yana magana kamar bai san abinda yake faruwa ba, kuma wannan duk makircin rahoton karya ne da maciya amana barayi suke kawo masa ya hau kai ya zauna

Har abada ina kaunar Shugaba Buhari, Wallahi maciya sun cuci shugaba Buhari, sun bata masa kyakkawan tarihinsa, kuma wai a hakan suke so ku sake zabarsu saboda ba mu da hankali

Allah Ka isar masa tare da mu gaba daya.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button