ƙarshen tika-tika, tik Ya Dawo Kannywood! Abinda Yasa Adam A Zango Yayi Mubayi’a ~ Afakallahu
HAUSAWA sun ce ƙarshen tika-tika, tik! A yau dai Adam A. Zango ya yi mubayi’a ga Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, ya yi rajista a matsayin ɗan fim mai gudanar da sana’ar sa a jihar.
Idan kun tuna, a baya jarumin ya kasance ɗaya daga cikin jarumai da mawaƙan da su ka ƙi amincewa da tsarin da hukumar ta yi na yin rijista ga duk wani mai sana’a a masana’antar Kannywood wanda ke harkokin sa a Kano.
Bijirewar da ya yi wa hukumar ya sa aka kusa kama shi a gurfanar da shi a kotu, bayan an hana shi wani taron saduwa da masoyan sa.
Zango ya yi fushi, har ya bayyana cewa shi ya ma fita daga Kannywood, ya maida harkokin sa Legas inda zai riƙa yin waƙoƙi a gidajen biki.
To sai dai bai daɗe da bayyana wannan ƙudirin ba aka shiga zaman dole sanadiyyar ɓarkewar cutar korona.
A yau Juma’a, 28 ga Agusta, 2020 jarumin dai ya je hedikwatar hukumar tace finaginan a Kano, inda ya maida fom ɗin rajista da ya saya kwanan baya, wanda har a lokacin ya ɗora hoton fom ɗin a Instagram bayan ya cike shi.
Bayan zuwan sa hikumar, Zango ya wallafa hotuna takwas da ya ɗauka a hukumar shi da shugaban ta da ‘yan rakiyar sa a Instagram tare da rubuta cewa komai ya yi farko zai yi ƙarshe, kuma ya dawo Kannywood gadan-gadan.
Wannan ya tabbatar da cewa yanzu dai jarumin kuma mawaƙi ya zama mai cikakken iko a masana’antar kamar sauran waɗanda su ka yi rajista.
Da ya ke yi wa mujallar Fim ƙarin bayani game da zuwan Zango hukumar a yau, shugaban hukumar, Alhaji Isma’il Na-Abba (Afakallahu), ya ce, “Adamu ya zo ya yi rajista ne yau Juma’a. Da ma tun can baya da ake rijistar bai zo ya yi ba.
“Ya kuma yi maganganu na fahimta, inda ya ce shi ba rigima ya ke yi ba, kuma duk abubuwan da aka ba shi ya yarda. A baya an ba shi abubuwa a baibai, don haka yanzu a shirye ya ke ya bi duk tsarin da hukuma ta ce.
“Kuma yanzu ya cigaba da harkokin sa kamar yadda kowane jarumi ya ke yi a Kano ba tare da wata tsangwama da sauran su ba.”
A kan abin da hukumar za ta ce game da wannan mubayi’a da jarumin ya yi, Afakallahu ya ce, “Ai ka san ita hukuma uwa ce, kuma uba ne, idan ɗan ta ya bijire mata za ta yi ƙoƙari ta dawo da shi kan hanya, idan kuma ya dawo kan hanya ba za ta ƙi shi ba, za ta ɗauke shi ta yi masa duk wani abu da za ta yi wa sauran ‘ya’yan ta.
“Kuma da ma manufar ba hana shi ba ne,manufar kuma ba a kan shi aka fitar ba ballantana a musguna masa ko a hana shi ko wani abu mai kama da haka. Manufar gyara ne da mutuntawa da kuma yadda za a gyara sana’ar ta haɓaka.
“Kuma ka ga yanzu, ka ga an yi nasara tunda ya fahimci tafiyar da ya ke yi ba ita ba ce daidai, ya zo ya bi tsarin doka na hukuma domin ya zauna lafiya kamar sauran ‘yan’uwan sa jarumai.”
Akwai mawaƙa da jarumai masu irin ra’ayin sa a baya, waɗanda har yanzu ba su je sun yi rijista ba.
A kan irin waɗannan, shugaban ya bada shawara kamar haka: “Shawara ta gare su shi ne, su gane cewa duk abin da hukuma ta yi, ta na yi ne domin masalahar al’umma, ba masalahar mutum ɗaya ba ko kuma kallon wani layi ɗaya. Ita doka ko gwamnati ta na kallon duka layuka, ta na kallon na mai yi, ta na kallon wanda ake yi domin shi, kuma sannan ta na kallon duk ɓangarori, hatta shi tattalin arzikin na al’umma.
“Ka ga dole ba za a kawo abin da zai gurɓata tunanin mutane ko addinin su ba ko kuma yanayin zamantakewar mu. Don haka abin da na ke kira gare su, su yi ƙoƙari su fahimci cewa bin doka shi ne zaman lafiya, bin doka shi ne zai sa kowa ya samu arziki mai ɗorewa da kwanciyar hankali. Rashin yin wannan zai zama mutum ba ya cikin kwanciyar hankali ko zai zama mutum ko zai zama ba ya cikin mutanen da za su samu arziki mai ɗorewa, saboda kullum ya na taraddadi, ya na zullumi zai taka doka, kuma doka ba za ta bar shi ba, kuma za ta taka shi.”





