A Jihar Borno Ma An Kubutar Da Wani Yaro Da Aka Killace Shi Na Tsawon Lokaci
An kubutar da wani yaro dan shekaru sha uku da haifuwa mai suna Aminu wanda aka ajiye shi a baranda a nan yake kwana komai zafi ko sanyi. Kuma sau daya suke ba shi abinci a yini, kamar yadda baban yaro ya shaidawa wadanda suka kubutar shi.
Aminu dai da mahaifin sa Malam Murtala da matansa suna zaune a titin Baga dake cikin Maiduguri.
Tun bayan sakin mahaifiyar Aminu da mahaifinsa ya yi aka ajiye shi a baranda na tsawon lokaci.
Kungiyar (National human rights commission) karkashin jagorancin Barista Jummai Mishelia ne suka kubutar da Aminu, inda yanzu Malam Murtala da matan sa suke hanun hukuma, yayin da shi kuma Aminu yake karkashin kulawar wadanda suka kubutar da shi, inda za su kai shi asibiti domin duba lafiyar sa
Hotuna: Junaid Jibril Maiva
Daga Real Sani Twoeffect Yawuri