Labarai

EFFC na bukatar majalisa tayi doka a kan masu zama attajirai dare guda a Najeriya

Sabon shugaban hukumar EFCC dake yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, Ola Olukayode ya bukaci majalisar dokokin kasar da ta samar da wata dokar da zata bai wa hukumarsa damar gudanar da bincike a kan mutanen dake yin arziki dare guda ba tare da sanin sana’ar da suke yi ba.

Olukayode yace idan majalisa tayi sabuwar dokar, zata taimaka musu wajen hukunta masu satar dukiyar jama’a da kuma zama attajirai dare daya.

Shugaban hukumar yace tuni wasu kasashe irinsu Birtaniya da Australia da Mauritius da Kenya da kuma Zimbabwe suka amince da irin wannan doka, wadda ta basu damar gudanar da bincike domin gano yadda irin wadannan attajirai suka tara dukiya ba tare da sanin kasuwancin da suke yi ba.

EFFC na bukatar majalisa tayi doka a kan masu zama attajirai dare gudaNajeriya
EFFC na bukatar majalisa tayi doka a kan masu zama attajirai dare guda Najeriya

Jaridar liberty tv na ruwaito cewa Olukayode yace wannan matsalar bah wai ta tsaya a Najeriya bane, ganin yadda kasashe da dama ke sabunta dokokin su domin tafiya da zamani da kuma dakile yadda ake halarta kudaden haramun.

Shugaban hukumar yace samar da irin wannan doka a Najeriya zai bai wa jami’an hukumarsa damar tinkarar irin wadannan attajiran dare daya da kuma gano inda suka samun dukiyarsu.

EFCC tace rashin samar da dokar da ake bukata, zai dakile kokarinsu na shawo kan matsalar cin hanci da rashawa wanda ke yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa.

Hukumar EFCC ta samu gagarumar nasara wajen kwato kadarorin da barayin gwamnati suka mallaka ba bisa ka’ida ba da kuma nasarar daure da dama daga cikinsu.

Irin wadannan kadarori sun hada da gidaje da motoci da jiragen ruwa da kuma filaye.

Cikin wadanda tayi nasarar daurewa harda tsoffin gwamnoni da ‘yan majalisu da kuma ministoci.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button