Labarai
Za a bude makarantu ga daliban da za su rubuta WAEC
Advertisment
Gwamnatin Najeriya ta amince a sake bude makarantu ranar 4 ga watan Agusta ga daliban da za su rubuta jarrabawar karshe.
Sanawar da mai magana da yawun ma’aikatar ilimi ta kasar, Ben Bem Goong ya fitar ranar Litinin, ya ce dalibai za su samu damar yin shiri na mako biyu domin rubuta jarrabawar WAEC wacce za a soma ranar 17 ga watan na Agusta.
Ya kara da cea an dauki matakin ne bayan taron da aka gudanar tsakanin jami’an ma’aikatar ilimi da kwamishinonin ilimi na jihohi 36 da kungiyar malaman makarantu ta kasa da kuma hukummin rubuta jarrabwa.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com