[Bidiyo] Wata mata A Borno ta kashe kanta bayan wani yayi mata fyade
AJihar Borno da ke Arewa maso gabashin Najeriya wata ‘yar gudun hijira da ke aiki a gidajen mutane don neman abun rufin asiri ta gamu da ajalinta, bayan da wani ma’aikacin agaji ya keta mata haddi a badalance, wanda hakan ya sa ta caka wa kanta wuka, ta mutu.
Yanzu haka dai jami’an tsaro sun kama wanda ake zargi da kasheta wanda shi kuma ya fadawa manema labarai cewa
“Ni bani nayi mata fyade ba kuma bani na kashe bata dalilin da yasa tana zuwa inda nake shiyasa kawayenta suke jifanta da kalma karuwanci to abun yayi mata zafi shiyasa taga bati tayi abinda zai fitar da ita daga wannan zargin kawaye.
Kuma daman aisha tana da zafin rai sosai wanda zata iya yanka kanta akan abinda bai kai ya kawo ba.”
Ga bidiyo nan zaku saurari cikakken bayyani da gidan rediyon voa hausa taskarvoa na dauko rahoto.