Kannywood

Waka Da Rawa Zai Maye Gurbin Manyan Jarumai A Kannywood ~ Sanusi Oscar 442

Fitaccen mai bada umarnin a fina-finai da wake-wake a masana’antar shirya fim ta Kannywood, Sunusi Oscar 442 ya ce sabon salon waka da rawa da a ka fito da shi a masana’antar, wata hikima ce da za ta maye gurbin wa su manyan jarumai a masana’antar ta Kannywood.
Cikin ganawar da ya yi a talabijin na Arewa24 ya ce babu magada da za su gaji manyan jaruman dake taka muhimmiyar rawa a halin da a ke ciki yanzu a masana’antar.

Wannan dalilin ne ya sanya Northflix ta tuntunbi Sunusi Oscar 442 domin jin karin bayani kai tsaye daga bangaren sa.

Wannan ya na nufin cewa kun kirkiri waka ne saboda sabbin jarumai su samu karbuwa kamar manyan jaruman dake masana’antar yanzu?
“Kusan haka ne kuma kusan ba haka bane, ita waka ta na da tasiri matuka a wajen al’umma, tun da harka ce da ake yin ta ta soyayya, ita kuma soyayya ba ta mutuwa saboda idan kai ka tsufa wani a lokacin yake tashi, shi ya sa za ki ga samari da ‘yan mata su ka karbi abun, kuma a baya an yi irin su, Ali Nuhu, Adam A Zango marigayi Ahmad S Nuhu da Sani Danja, kuma dukkan wadan nan sun samu fifikon karbuwane saboda waka da su ke yi a fim, wanda ko talla ne a ka kawo daga manyan kamfanunuwan dake kasar nan dama kasashen waje, to su a ke dauka a ba su dama domin wakar nan ta sa sun fi kowa shiga gidajen mutane.

 Za ki ga ko ina su ne sun san sauran jaruman da sun iya aktin din ma fiye da su irin su Momo, Alhassan Kwalle da sauran su, ba don komai ba sai don banbancin waka“.
Amma ka na ganin a cikin wadan nan sabbin jaruman akwai wanda zai iya taka muhimmiyar rawa ya kuma bada gudunmawa a masana’antar kamar yadda wadan can na baya su ka bayar?
“Ai babu wani abun da za a ce ba za a samu wanda ya fi shi ba, babu shi a rayuwar  duniya, Allah ne kawai daya, amma duk wani jarumi da ki ka sani an yi shi, kuma za a yi wanda zai goge shi ya goge shafin sa ya kuma bude sabon shafi, mu ma daraktoci dole mu na zaune haka zamu matsa mu bawa wadanda su ka fimu gwanancewa dama a kafa sabon abu, ba laifi bane cigaba ne, kuma sai ta yi wu a kasan ka yake ko karkashin ka, amma matukar ya fika sa ni dole ka matsa ka bashi waje, domin a samu cigaban da a ke nema, a yanzun ma akwai da yawa da ba a ankara da su ba, wadanda idan a ka ce za a gwada su to za su bada mamaki za kuma su doke da yawa a cikin jaruman da a ka san da su din. Ina nufin za su iya gadon tsoffafin jaruman, ba sabon abu bane gadon wani tsohon jarumi a masana’antar Kannywood, sai dai kawai mutum ya ce kila ka fi tsawan rai ko kuma yadda harkar ta karbu a baya, tun da yanzu za’a iya cewa an samu tsaiko na ci gaban masana’antar, amma ba wai a ce ba za a iya wuce mutum ba, su ma wadanda su ka zo na farko-farkon gani a ke baza a iya samun wadan da za su doke su ba , tun da daga farko an fara da irin su Dan Haki, Karkuzu, Samanja da sauran su, sai kuma a ka zo a ka samu irin su Ibrahim Mandawari, Shehu Hassan Kano da Iyantama, sai kuma a ka zo kan su Alhassan kwalle, Aminu Acid da sauran su, sai kuma a ka zo kan su Ali Nuhu, Adam Zango da sauran su. Sannan kuma yanzu an kawo zunzurutun samari kuma yanzu haka akwai wajen mutum bakwai ko takwas su na nan da a ke fafatawa da su, sannan kowannen su ya na bakin kokarin sa, kuma su na yin abubuwan da yafi na ‘yan bayan, sai dai karfin na bayan ya saka ba a gani wannan kuma dama sai sannu a hankali“.

Amma kuma akwai jarumai irin su Maryam Yahaya, Hassana Muhammad, Umar M shariff da dai sauran su wadanda yanzu su ke tasowa, domin maye gurbin wadancan jarumai, sannan kuma su ba waka a ka yi mu su ba su ka karbi bu, mai za ka iya fada a kan wadannan?

“Jarumai irin su Hassana Muhd, Maryam Yahaya, Zee Preety, Bilkisu Shema, Bilkisu Abdullahi Amal, Umar da sauran su, ba za mu cika baki a kan su ba, amma daga wajen mu su ka fara, mu ne wadanda mu ka taimaka su ka taso, kai wancan lokacin da su wadan nan su ka gansu kuma su ka janye mana su, mu na da tarihin komai tun da mu mu ka yi , ba wai mu na bakin ciki bane da abun da yake faruwa ba, domin dukkan mu daya ne su din namu ne mu ne mu ka fara kafa su, Northflix na ruwaito.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button