Labarai
Ina jin dadin yiwa tsoffin mata fyade ~ Sani Garba da aka kama da yiwa ‘yar shekaru 60 fyade a jihar Naija
Advertisment
Sani Garba dan shekaru 32 da aka kama da zargin yiwa wata tsohuwa fyade a Suleja dake jihar Naija ya bayyana cewa yana jin dadin yiwa tsaffin mata fyade.
Ya bayyana cewa matar ta dauki hankalinshi ne saboda yanda take juya mazaunanta idan tana tafiya. Yace amma yna neman afuwa.
Ya kara da cewa rashin kudi da zai kula da budurwa ne yasa yake bin tsaffin mata yana musu fyade inda yace yawa tsaffin mata 3 fyade. Yace shima abin na damunsa, wani lokacin sai ya tsaya ya tambayi kansa wai menene matsalarsa?
Me magana da yawun ‘yansandan jihar, Wasiu Abiodun ya bayyana cewa za’a gurfanar da wanda ake zargin a Kotu.
Advertisment
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com