Kannywood
Kasuwaci : Duniya Ta Chanza Amma Kannywood Basu Gane Ba ~ Sani Mu’azu
Advertisment
KWANAN nan aka naɗa tsohon shugaban ƙungiyar ƙwararru masu shirya finafinan Hausa, wato Motion Picture Practitioners Association of Nigeria (MOPPAN), Alhaji Sani Mu’azu, sarautar Mai’unguwa a unguwar da ake kira Ali Kazaure, cikin Jos, babban birnin Jihar Filato. Idan ba ku manta ba, shi ma fitaccen jarumi Ibrahim Mandawari shi ne mai’unguwar Mandawari cikin birnin Kano a yanzu haka.
Wannan ya na nuni da cewa ‘yan fim ɗin Hausa mutane ne masu daraja a cikin al’umma, akasin kallon da wasu ke yi masu. Domin ban da waɗannan biyun ma, akwai wasu ‘yan fim ɗin da ke riƙe da muƙamai a masarautu da dama.
Alhaji Sani, wanda fitaccen darakta ne, furodusa kuma jarumi, ya yi wa mujallar Fim bayanin yadda aka yi ya samu wannan muƙami da kuma wani muƙamin wanda da ma can ya na riƙe da shi kafin wannan. Haka kuma mun yi amfani da wannan dama don jin ra’ayin sa a kan makomar Kannywood, musamman ta fuskar kasuwanci da sababbin hanyoyin fasaha su ka sauya a wannan zamani, da kuma batun siyasa, ganin cewa ya fito a matsayin gwamna a shirin ‘Kwana Casa’in’ na gidan talbijin na Arewa24. Ga yadda hirar ta kasance:
FIM: Me za ka ce game da wannan muƙami da ka samu na mai’unguwa?
SANI MU’AZU: Alhamdu lillah. Shugabanci na Allah ne, ban taɓa neman in zama mai’unguwa ba; an zo zaɓen mai’unguwa ne, mutane su ka ga na cancanta, su ka ce ya kamata in fito in nema. Ko da yake takara aka yi, saboda akwai ma wasu da su ka nema, amma Allah ya sa na ci. Kuma da ma can ina da sarauta a kai na ta Galadima.
FIM: Menene burin ka a matsayin shugaban al’umma, musamman yadda zama ya kan yi tsami tsakanin Hausawa da wasu ƙabilu a garin Jos?
SANI MU’AZU: Babu wani buri da ya wuce yadda za mu ƙarfafa zaman lafiya a tsakanin mu. Allah ya riga da ya haɗa mu zama wuri ɗaya, kuma an yi shekaru aru-aru ana zama tare.
A ‘yan shekarun baya an samu rashin jituwa, amma da aka haife mu a nan, aka haifi iyayen mu a nan, mun san akwai wani lokaci da aka yi zama na amana da zaman lafiya, kuma an samu cigaba a wannan lokacin. To, ƙoƙarin mu ya za a yi mu dawo da wannan zaman lafiya da aka yi a baya. Sannan kuma mu wayar da kan mutane. Shi ya sa a harkoki na, duk harkar da na ke yi ban da harkar fim na maida hankali a kan ‘peace education’.
Don ma na fahimci abin da na ke yi, har na je Ghana, Kofi Annan International Peacekeeping Training Centre, inda na yi kwas a kan ‘Peace Education’ ɗin, kuma tun da na dawo duk rubuce-rubuce na, musamman a soshiyal midiya da sauran su, za a ga cewa na karkata a kan yadda za a kawo zaman lafiya, ba a Filato ba, a Nijeriya ma baki ɗaya.
FIM: Shin ko Kannywood za ta amfana da wannan sabon muƙamin naka?
SANI MU’AZU: To, ai Kannywood ta amfana! A ce ɗaya daga cikin shuwagabanni na Kannywood ya samu muƙami, ai Kannywood ce ta samu muƙamin.
Idan da a ce Kannywood ba a martaba ta ko ba a ganin girman ta ko ba a yarda da abubuwan da ake yi ba, da babu shakka in Kannywood ta na da tabo, da ya shafe ni. Amma in an ba ni, an ba Kannywood ne. Don haka Kannywood ce ta samu wannan shugabanci da na samu.
FIM: Me za ka ce ga masu raina ‘yan fim, bayan ga ka ka zama shugaban al’umma?
SANI MU’AZU: Ga masu raina ‘yan fim zan bar su, in yi mana magana mu ya mu ‘yan fim. ‘Yan fim suna mu ka tara; akwai da yawa da su su ke janyo mana wannan rainin, kuma ɗan’adam zai iya martaba kan sa, kuma zai iya wulaƙantar da kan sa. Kyan mutum a san shi bisa ga sana’ar sa. Wanda ya riƙe sana’ar, ita ma za ta riƙe shi, wanda kuma ya banzatar da sana’ar, babu shakka zai wulaƙanta shi ma in ba ya shiga taitayin sa ba.
Ga waɗanda kuma su ke yi mana kallo daga waje, su gane cewa ba mu taru mun zama ɗaya ba. Mu da mu ka assasa wannan masana’anta mun ɗauki harkar fim sana’a ce, kuma sana’a da mu ke yi tsakani da Allah. Kuma wasun mu duk da za a tambaye mu neman Aljanna mu ke yi da wannan sana’ar, ba neman kuɗi ba. Saboda haka a kyautata mana zato, a yi mana addu’a. Idan an ga mun yi kuskure, a yi mana addu’a mu dawo kan hanya.
FIM: ‘Yallaɓai, ganin yadda harkar fim ta shiga cikin garari, kusan ana iya cewa harkar ta durƙushe. A matsayin ku na shugabanni a masana’antar, wane ƙoƙari ku ke yi don ganin kun dawo da martabar harkar?
FIM: Na farko dai ba sana’ar (fim) ce kaɗai ta canza ta ke da matsaloli ba, duniyar ce gaba ɗaya ta canza. Don haka duk wanda ya ke nazarin abubuwa ya san an samu canji na yanayi, ba a nan Kannywood ba, a duniya ne baki ɗaya. ‘Technology’ ya canza mana akalar kasuwar mu. Amma yawancin ‘yan kasuwar mu ba su fahimci yadda abin ya ke ba, da yake a zamanance ne abubuwan su ka zo su ka canza abubuwa.
A yau ka saida kaset ko ka saida sidi ba zai yiwu ba, saboda wannan hanyar ta isar da saƙo an yi waje da ita. Babu ita, kuma ba za ta dawo ba. Su kan su ‘CD player’ ɗin ma an yi waje da su; yanzu in ka je shago za ka ga ba saida su ake yi kamar da ba, masu sayen nasu ma sun daina saya. In ka je gidaje da yawa ba za ka tarar da VCD ko wani DVD ba yanzu.
Komai ya canza, am
ma kamar mu ba mu farga ba, mu na ta tunanin kamar za a koma ne ana harkar sidi. Wannan ya na ci mana tuwo a ƙwarya, don haka dole mu farka.
ma kamar mu ba mu farga ba, mu na ta tunanin kamar za a koma ne ana harkar sidi. Wannan ya na ci mana tuwo a ƙwarya, don haka dole mu farka.
Na biyun su, tsarin kasuwancin ma ya canza. Yanzu an koma ta intanet ake yin abubuwa. Manyan ‘yan kasuwa a intanet su ne masu samun maƙudan kuɗi. Ka dubi irin waɗannan da su ke saida hajojin su ko’ina a duniya, yanzu su na samun ‘turnover in billions’. Wannan alama ce ta cewa duniyar ta na canzawa.
Yanzu ka dubi Netflix, su harkar fim su ke yi, kuma ta ‘the same internet’ su ke yi. A yanzu sun zama gagarabadau, Hollywood ma ta na jin tsoron su, ballantana sauran ƙananan industiri. Alama ce ta cewa duniyar fim ɗin ma ta na canzawa.
Lallai in mu na so mu samu maslaha, mu samu yadda za a gano bakin zaren, sai mun fito da tsarin da za mu zamanantar da masana’antar. Shi yin fim ka fito da labarin da zai taɓa zuciyar mutane har a gani a saya. Babu ranar da za a daina son a ga sabon labari. Ɗan’adam ya na son duk abin da zai yi, ya samu lokaci na nishaɗi. Matsalar kasuwar hanya da za mu kai ga wanda ya ke so ya yi wannan nishaɗin. In ba mu yi nazarin hanyar cimma kasuwar tamu ba, ba za mu fita daga cikin wannan tsari ba.
Amma kuma abu ne da ya ke buƙatar ilimi. Da ya ke kuma a zamanance ne, sai mun nemi ƙwararru mun jawo su.
Kasuwanci na zamani ba irin kasuwancin da mu ke yi a Ƙofar Wambai ko Singa da sauran su ba ne. Kasuwanci ne yanzu da za a yi shi ta intanet; za a yi amfani da kwamfutoci da sauran su. Sai mun nemo ‘yan kasuwa waɗanda za su iya yin kasuwancin hajar mu a cikin tsari na zamani. Ni a wuraren da na maida hankali kenan.
FIM: Ka fito a matsayin gwamna a cikin shirin ‘Kwana Casa’in’. Ko wannan ya zaburar da kai ka nemi takarar siyasa a Jihar Filato?
SANI MU’AZU: A’a, ni ban yarda da siyasa irin ta jam’iyya ba. Kowane ɗan’adam ya na siyasa, kuma an ce “man is a political animal”. Amma ni a fahimta ta, siyasa irin ta jam’iyya ba ni da sha’awa.
Na taɓa gwadawa a baya, sai na ga akwai ƙazanta da yawa a ciki. Tun da na ƙyamaci abin da ya shafi siyasa ta jam’iyya, sai na yi ƙoƙari na kuɓutar da kai na daga batun abin da ya shafi siyasa ta jam’iyya. Ko wannan muƙamin da na samu na mai’unguwa, da ina siyasa ba zan samu ba.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com