Labarai

Labari Mai Dadi : Sama Da ‘Yan Nijeriya 250,000 Za Su Samu Aikin Yi A Sabon Shirin Da Buhari Ya kaddamar A Yau

Advertisment

Sama Da ‘Yan Nijeriya 250,000 Za Su Samu Aikin Yi A Sabon ShirinHarkar Gwal Da Shugaba Buhari Ya Kaddamar A Yau

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, 16 ga watan Yuli, ya jagoranci wani taro na yanar gizo inda ya kaddamar da shirin fadar shugaban kasa na bunkasa hakar gwal (PAGMDI).

Rahotanni sun bayyana cewa, shirin PAGMDI, zai samawa ‘yan Nijeriya akalla 250,000 ayyuka, yayin da gwamnatin tarayya za ta rinka samun kudaden shiga $500m a kowacce shekara.

A cewar wata sanarwa daga Femi Adesina, mai tallafawa shugaban kasa ta fuskar watsa labarai, shirin zai taimaka wajen kawo karshen hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba da kuma baiwa Nigeria kwarin guiwar samun makoma mai kyau a nan gaba.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button