Buhari: Abubuwan da shugaban Najeriya zai yi a ziyararsa ta jahar Borno a Yau
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai kai ziyara jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar a ranar Alhamis.
Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da gwamnan jihar Borno ya fitar mai sa hannun mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai Isa Gusau.
Kamar yadda Bbchausa na ruwaito. Borno ce jihar da ta zama hedikwatar ƙungiyar Boko Haram inda ake fama da hare-haren mayaƙan.
Gwamna Babagana Umara Zulum ya roƙi ƴan jihar da su ba da goyon baya da fatan alheri a yayin ziyarar.
“Ina sake gode muku kan goyon bayan da kuka bai wa gwamnatin nan. Ina godiya bga kowa da kowa, kan goyon bayanku da fatan alherinku da addu’o’i da kuma zamantowarku ƴan ƙasa na gari,” kamar yadda sanarwar ta ce.
Lokaci na ƙarshe da Shugaba Buhari ya kai ziyara Borno shi ne ranar 12 ga watan Fabrairun 2020, inda har wani dandazon mutane suka yi wa shugaban ihun ”ba ma yi, ba ma yi”.
Daga cikin dalilan ziyarar Shugaba Buhari Borno a wannan karon kamar yadda gwamnatin jihar ta faɗa akwai.
Shugaba Buhari zai kai ziyarar ne don duba yanayin tsaron da yankin arewa maso gabas ɗin ke ciki. Sannan zai ƙaddamar da wasu ayyukan ci gaba da gwamnatin jihar ta gina
Shugaban zai kuma ƙaddamar da rukunin farko na gidaje 10,000 waɗanda ya amince da gina su tare da samar da kuɗaɗen yin su, don sake tsugunar da ƴan gudun hijira.
“Ina farin cikin sanar da ku cewa gwamnatin tarayya ƙarƙashin Shugaba Buhari ta kamma gina gidaje 4,000 cikin 10,000 da aka amince a gina wa ƴan gudun hijira.
“Wasu daga cikin gidajen nan suna yankin Kaleri da Dalori da sauran wurare,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta ƙara jaddada gamsuwarta kan yadda “gwamnatin Buhari ta shawo kan matsalar tsaron sosai, ba kamar yadda abin yake a baya ba.”
“Gina waɗannan gidaje ya ta’allaƙa ne ga samun zaman lafiyar da aka yi a yankunan jihar Borno.
“Na san har yanzu muna fama da matsalar tsaro, amma kuma idan muka waiwaya baya za mu ga cewa an samu sauƙi musamman a yadda a baya wasu yankunan ma ba a shigarsu,” in ji sanarwar.
Sai dai duk da wannan yabo da gwamnatin jihar Borno ta yi wa gwamnatin Buhari, masu sharhi na ganin da sauran rina a kaba sosai a yaƙin da ake a ƙoƙarin daƙile ƙungiyar Boko Haram.
A watan Fabrairun 2020 ne Shugaba Buhari ya kai ziyara Borno, inda har wani dandazon mutane suka yi wa shugaban ihun ”ba ma yi, ba ma yi”.
Hakan kuma ya faru ne lokacin da Buhari yake barin fadar Shehun Borno zuwa gidan gwamna a wani waje da ake cewa ‘Yan Nono.
A lokacin Buhari dai ya ziyarci Maiduguri ne domin jajanta wa gwamnati da al’ummar jihar bisa hare-haren da Boko Haram ta kai kan wasu matafiya abin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.
Sai dai Kakakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya ce, wanda ya dauki bidiyon da ya bazu a shafukan intanet da ke nuna ana yi wa Buhari ihu bai a yi wa mutanen Borno adalci ba — wadanda ya ce an san su da karamci da son baki.
“Da ni aka shiga gari [Maiduguri] tun daga filin jirgin sama zuwa fadar Shehun Borno kuma jama’a ne suka fito suna cewa sun gode suna ala san barka.”
“Amma akwai wata matattara da suke cewa ba sa so, kuma ni ma na ji da kai na masu cewa ba sa so,” in ji Garba Shehu.