Hatsarin Bokaye Da Matsafa A Cikin Al’umma ~ Sheikh Aminu Ibrahim daurawa Kano
MANZON ALLAH SAW YACE: DUK WANDA YAJE WAJAN BOKA KO ƊAN TSUBBU (MAI BADA LABARIN ABINDA YA WUCE KO KUMA ABINDA ZAIZO NAN GABA) ALLAH BA ZAI KARƁI SALLAR SA BA TA KWANA 40.
MANZON ALLAH SAW YACE :DUK WANDA YAJE WAJAN BOKA MAI DAAWAR YASAN GAIBU, YA KUMA GASKATA SHI ACIKIN ABINDA YA BASHI LABARI, HAƘIƘA YA KAFURCEWA ABINDA AKA SAUKARWA ANNABI SAW.
ABUBUWAN DA SUKE KAI MUTANE WAJAN BOKAYE,
NA ƊAYA, NEMAN WANI MAGANI NA WATA CUTA DA TA GAGARA
NA BIYU, NEMAN MALLAKAR MIJI KO MATA
NA UKU, RABA TSAKANIN MASOYA KO MAAURATA. KO IYAYE
NA HUƊU, NEMAN MULKI KO KUƊI.
NA BIYAR, KORAR KISHIYA KO HAUKATATA.
NA SHIDA, NEMAN MIJI KO KORAR ALJANNU.
NA Bakwai, NEMAN A KASHE WANI KO A HAUKATA SHI.
1 BOKA SHINE MAI DAAWAR YASAN GAIBU, KO ƘARYA YA KEYI KO KUMA YANA MU’AMALA DA ALJANNU.
2.YIN SIRKULLE, DA KARANTA ABUBUWAN DA BAA FAHIMTA.
3. DUK WANDA YAKE TSAKUƊA AYOYI DA ƊALASIMI
4. NEMAN A YANKA WATA DABBA TA MUSAMMAN BAƘA KO FARA
5.TAM BAYAR SUNAN MAHAIFIYA.
6. NEMAN WANI ƁANGARE NA JIKIN MUTUM, KAMAR GASHI KO FARCE
7. NEMAN WANI TUFAFI DA MUTUM YA SANYA A JIKIN SA.
8. NAMAN KAƊAITA DA MUTUM IDAN YANA CIKIN JAMA’A
9. KARANTA ABUBUWAN DA BAA GANEWA.
10. NEMAN AJE AGA INDA KAKE KWANA KO INDA KAKE SANAA.
11. NEMAN A BINNE WANI ABU A GIDAN. MUTUM KO GIDAN TURURUWA, KO KAN HANYA
12. RASHIN YIN SALLAMA KO HANA YIN SALLAH A GURIN SA
13. HANA KA YIN WANI ABU DA SHARI’A TA UMARCEKA NA FARILLA KO WAJIBI.
UMARTAR MUTUM DA YA ZAUNA CIKIN ƘAZANTA KO YA KARANTA WANI ABU DA BAYA FAHIMTA.





