Dalilin Da Yasa Nayi Waka AKan Matsalolin Fyade (Rape) ~ SadiQ zazzaɓi
A daidai lokacin da kungiyoyi da kuma daidaikun mutane su ka ta shi domin fadakarwa a kan matsalolin keta hakkin mata musamman kananan yara wanda a yanzu ya zama ruwan dare a kasar nan. Shi ma fitaccen mawaki Sadeek Zazzabi ya fitar da sabuwar waka, domin ya bayar da ta sa gudummawar a matsayin sa na mawaki. Wakar dai an tsara ta ne a wani tsari da kuma salo da ya ke tafiya da hankalin mai ji da kuma kallo, musamman yadda a ka yi amfani da taron gangami na mutane dauke da kyallaye da kuma kwali an yi rubuce-rubuce a kan kyamatar fyade, yayin da kuma a wani bangaren a ka yi amfani da zaman Kotu inda shi Sadeeq Zazzabi ya fito a matsayin lauya, duk dai a cikin wakar. Mun tambaye shi dalilin sa na yi wakar a cikin wannan salon da kuma sakon da ya ke son isar wa, inda ya bayyana mana cewar.
“To ni dai daman mawaki ne da ya ke fadakarwa, kuma na ke so na fadakar da irin basirar da Allah ya ba ni da na ke so, al’umma su amfana da ita, kuma al’umma ba za su amfana ba sai irin sakon da ka zo mu su da shi zai amfane su wajen fai’dantuwa da abubuwa. To a na cikin wani yanayi da harkar fyade ta ta’azzara, kuma abu ne wanda ni tun tasowa ta na ke jin sa, kuma ya ki karewa. To a matsayi na mawaki, sai na ga ni ma ya kamata na yi wani kira, da wayar da kai dangane da yadda za a kare kai, domin haka na shirya wakar fadakarwa da al’umma”.
Mun tambaye shi dangane da irin salon da ya zo da shi a cikin wakar, musamman shiga irin ta lauyoyi da ya yi har kuma a ka yi amfani da Kotu.
Sai ya ce”To ka san waka idan za ka yi ta bidiyo, ta na da salo da kuma tsari, domin haka sai ka nemi tsarin da za ka yi wanda ya dace da wakar. Domin haka waka ce ta fyade, wanda a ke ta korafi a kan sa, domin haka sai mu ka ga ya dace mu yi ta a Kotu, saboda akwai abubuwa da yawa a kan abun da ya shafi fyade wanda a ido ba za ka iya nuna shi ba. Maimakon gyara idan ka ce za ka nuna abun da ya ke faru a bidiyo, to maimakon gyara sai kuma ka yi barna, saboda sai mu ka ce bari mu yi abun a takaice yadda jama’a za su fahimta, domin haka sai mu ka yi ta a Kotu, ga Alkali ga lauyoyi da su ke kare ma su laifi da kuma wanda a ka yi wa laifi. Ni na fito a matsayin Lauya wanda ya ke kare wadanda a ke cin zarafi, saboda haka sai a ka samar da Alkali, lauyoyi da wadanda a ka ci zarafin su da kuma wadanda su ka aikata abun, amma kuma duk da haka bai hana a haska maka wani bangare na abun da ya ke faruwa a kan fyade ba, saboda haka mun yi haka ne domin Jan ra’ayin ma su kallo domin isar mu su da sakon cikin nishadi”.
Ganin cewar a yanzu abubuwan sai kara yawaita su ke yi, ko wacce hanya za ka bi wajen isar da sakon ya shiga har cikin kauyuka?
“To ka san yanzu abubuwa sun sauya ba kamar a baya ba, da akwai kasuwa ta C D. Amma dai yanzu ba za ka ce kasuwar babu ita ba, sai dai ba kamar a baya ba, domin babu kaso Casa’in da biyar cikin dari na kasuwar, domin haka a yanzu hanyoyin isar da sakon a yanzu shi ne kafofin isar da sako na zamani, domin haka a yanzu zai zama har inda ma ba ka tunani sakon ya na zuwa, kuma magana ta gaskiya ita waka duk yadda ka kai ga isar da sako, to akwai wajen da ba za ta je ba, sai dai ka yi iya yin ka, wanda ya samu ya samu, domin haka idan mu ka ce sakon zai shiga ko ina da ina to mun yaudari kan mu. Amma dai in dai an yi abun yadda ya dace, to kwalliya za ta biya kudin sabulu”.
To menene fatan ka na gaba?
“Kamar dai yadda na fada maka har kullum ina fatan na ga na zama mawakin da ko ba a koda yaushe ba ya zamana ina yin wakoki na fadakarwa, ni dai babban sako na shi ne ita wannan wakar, Allah ya sa ta amfanar da al’umma. Ma su yi kuma Allah ya yaye musu, su kuma iyaye su kara yin taka tsantsan wajen kulawa da ‘ya’ yan da a ka haifa ta hanyar kula da mutanen da su ke mu’amala da su, ina su ke zuwa, ina za su je. Muna fatan hakan ya zama izina ga iyaye, wajen kara kulawa da rayuwar yaran su”. A cewar Sadeek Zazabi.





