Kannywood

Yadda na samu kaina a cikin shirin Kwana Casa’in – Abba John

Advertisment

Duk wanda yake kallon shiri mai dogon zango na Kwana Casa’in ba zai kasa sanin fitaccen jarumi Abba John ba, saboda irin rawar da ya taka a cikin shirin.

To sai dai a lokacin tattaunawar su da wakilin mu jarumin ya bayyana mana yadda ya samu shiga cikin shirin da kuma irin yadda ya ji dadin samun nasarori da dama bayan ya kasance cikakken jarumi.
Amma dai ya fara gabatar da kan sa ne kamar haka.

“Ni suna na Abba Sa’ad kuma ni dan asalin garin Samunaka ne ta jihar Kaduna, sai dai tun ina karami mu ka dawo garin Kaduna da zama, domin haka a nan na yi rayuwa ta har zuwa yanzu duk wani fadi tashi na rayuwa a garin Kaduna na yi shi”.

Dangane da yadda ya gudanar da fadi tashin sa na rayuwa kuwa cewa ya yi.

“Tun ina dan karami ni mutum ne mai son gwada abubuwa da yawa a rayuwa a kan haka na yi aiki a Cafe sannan na fara gajerun fina-finai na barkwanci, kuma na yi waka”.

Dangane da yadda ya samu kan sa kuwa a cikin Kwana Casa’in Abba John cewa ya yi.

“Tun da farko na fada maka na yi waka to akwai wani aboki na mawaki ne sai ya samu gayyata za a yi hira da shi a Arewa 24, to sai ya fada mini, kuma daman idan za a yi hira da mawaki a na son a dan samu Gayu da za su zauna a na dan nuna su, to sai na yi kokari na halarci wajen. Bayan an gama hirar sai na karbi lambar wayar Nomiis Gee, to a haka ne mu ka fara magana da shi har na nuna masa ina sha’awar fitowa a shirin Dadin Kowa, sai su ka ce ai shirin ya yi nisa, amma dai akwai wani shirin da za a fara nan gaba kadan sunan sa Kwana Casa’in, in za a fara tantancewa sai ka zo. Haka kuwa a ka yi da za a fara tantancewa sai a ka sanar da ni na zo Kano kuma Allah ya sa na yi nasara”.

Ko daman kafin ka fara ka taba yin wani fim a cikin masana’antar fina-finai ta Kannywood?

“Gaskiya ban taba yi ba, sai daga baya ne ma a ka gayyace ni wani aiki, amma dai har yanzu ba a fara ba, domin haka zan iya cewa ban taba yi ba”.

Ya ya ka samu kan ka a matsayin jarumi a shirin Kwana Casa’in?

Gaskiya na ji dadi kuma ina yin alfahari da hakan, domin kuwa wata nasara ce babba a gare ni”.

Wane sako ka ke da shi ga masoyan ka?

“To masoya na ina yi mu su fatan alheri, saboda irin nuna kauna da su ke yi a gare ni, domin haka ina tare da su a koda yaushe kamar yadda su ma su ke tare da ni nagode Allah ya bar zumunci”. A cewar Abba John.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button