Uncategorized

Abu kamar wasa: Wani Matashi Ya Auri Budurwar Da Ya Hadu Da Ita a Twitter (Kalli Zafaffan Hotunansu)

Wata Baiwar Allah ta bayyana yadda ta hadu da Angonta a shafin Twitter a shekarar 2019

– @aysha_yayari ta fito da hotunan aurenta da Saurayin da su ka hadu a kafar sada zumunta

– Ba wannan ba ne karon farko da dandalin sada zumuntan zamani su ka hada aure a kasar

Wata Baiwar Allah mai suna Nana Aysha Yayari, ta bada labarin yadda haduwarta da wani Matashi a kan shafin sada zumunta na zamani ya kai ga sanadiyyar aurensu.

Soyayyar wannan Matasa ya fara ne kamar wasa a shafin Twitter, inda Malam Hassan Muazu ya lallaba a asirce ya aika mata da sakon sirri watanni kimanin 18 da su ka wuce.

Yanzu labarin wadannan Masoya ya zagaye gari bayan Aysha Yayari ta bayyana yadda Twitter ya hada ta da Masoyinta. A karshen makon jiya lamarin ya kai an daura masu aure.

A ranar Asabar 20 ga watan Yuni, 2020 Hassan Muazu ya auri Sahibarsa Aysha Yayari. Amaryar ta ce sun fara haduwa ne shekara daya da rabi, yanzu ga shi sun zama mata da miji.

Muazu Hassan da Aysha Yayari Hoto: Twitter
“Watanni kimanin 18 da su ka wuce, wannan Matashi ya aiko mani sakon DM da karfe 7:00 na safiyar wata ranar Asabar (shin, wa ke turawa Budurwa sako da sassafe haka a ranakun hutu)

Amarya Nana Aysha, ta kara da cewa: “Yau ga shi ina auren wannan mutumi, kuma babu abin da ya fi hakan farin ciki.” A karshe ta kara da godewa Ubangiji; Ta ce: “Alhamdulillah❤️.”

Kusan mutane 30, 000 su ka nuna sha’awar wannan labari a Twitter, su ka rika aikawa Ma’aurantan sakonnin taya murna da Ubangiji ya ba su zaman lafiya da zuri’a mai albarka.

Muazu ya nuna cewa tun farkon da ya fara zura idanunsa a kan kyakkyawar amaryar ta sa a yau, ya ke tunaninta, a karshe ya yi nasarar yin caraf da ita a matsayin mai dakinsa.

Yup. You’ve been first thing on my mind in the morning since Day 1… ❤️ https://t.co/uhFkmRZFPc

— Hassan! (@Hassan_Muazu) June 20, 2020

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button