Labarai

WATA SABUWA: Buhari Ya Amince A Gudanar Da Bincike Kan Shugaban Hukumar EFCC, Ibrahim Magu

Advertisment

Fadar shugaban kasa ta bayar da umarnin a soma bincike shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu, kamar yadda Jaridar Desert Herald ta rawaito.

Hakan na zuwa ne bayan Ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin Nijeriya, Abubakar Malami SAN, ya zargi shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arziki zagon-kasa da aikata laifuffuka a ofis.
Majiya daga fadar shugaban kasar ta bayyanawa jarida cewa shugaba Buhari ya yi na’am da maganar fara binciken shugaban hukumar ta EFCC, har kuma ta kai ana maganar Magun ya ajiye aiki.

Desert Herald ta ce akwai yiwuwar Ibrahim Magu ya sauka daga kan kujerarsa domin a yi bincike a hukumar EFCC, wannan zai bada damar Mohammed Umar Abba ya dare kan kujerarsa.

Advertisment

Mohammed Umar Abba shi ne babban darekta a hukumar wanda zai rike kujerar rikon kwarya bayan Magu.

A karshe ana tunanin Kwamishinan ‘yan sanda, Bala Ciroma ne zai zama sabon shugaban EFCC. CP Bala Ciroma Kwamishinan ‘yan sanda ne a babban birnin tarayya Abuja, kuma ya na cikin wadanda Abubakar Malami ya kai sunansa gaban shugaban kasa.
Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci a nada kwamiti da zai binciki Magu ne saboda nauyin zargin da Ministan shari’a ya jefe shi da su, sai dai shugaban kasar ya na gudun daukar matakin gaggawa.

Shugaba Buhari zai tabbatar ya nada kwamiti mai karfi da zai binciki zargin badakalar da ke kan hukumar domin a bi diddigin lamarin.
Fadar shugaban kasa ba ta tabbatar da hakan ba tukuna. Wanda ya samu masaniya ya ce tsohon alkalin babban kotun daukaka kara, Ayo Salami ne zai jagoranci kwamitin binciken.

Sauran ‘yan kwamitin sun hada da mai ba shugaban kasa shawara kan harkar tsaro. Shugabannin hukumar DSS, NIA da Sufetan ‘Yan Sanda da kuma Ministan shari’a su na cikin wadanda za su yi wannan bincike, za kuma su aikawa shugaban kasa rahoto nan da makonni biyu.

Da aka tambayi Mallam Garba Shehu game da lamarin, ya nuna cewa bai da labari Haka zalika jaridar ba ta yi nasarar tuntubar mai magana da yawun bakin EFCC, Dele Oyewale ba.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button