Advertisment
Shahararren dan wasan kwallon kafa na duniya, Paul Pogba, ‘yan jarida sun tambaye shi,
Me yasa ka ture kwalbar giya, ka dageta daga gaban ka a lokacin da ake tattaunawa da kai a gidan TV?
Sai Yace:
“Saboda ni Musulmi ne, an hana mu shan giya a Musulunci, bana so, bana sha, kuma bana so duniya ta ganni a matsayin mai shan giya bayan Annabin mu ya hana”.
Allah Ka albarkaci rayuwa Paul Pogba, Allah Ka tabbatar da shi da mu a cikin Musulunci Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum.