Addini

Nasihar Sheikh Kabiru Gombe Zuwa Ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

Advertisment

Jajirtaccen Malamin addinin Musulunci na Afirka baki daya Sheikh Dr Kabir Haruna Gombe ya sauke nauyin da Allah Ya daura masa na yin nasiha da fadakarwa zuwa ga shugaba Buhari da duk wani shugaba a Nigeria

Malam yace:
Muhammad Buhari kiwo  Allah Ya baka a Nigeria, kuma Allah sai Ya tsayar da kai a gabanSa ranar tashin Al-Qiyamah ya tambayeka hakkinmu mu ‘yan Nigeria, sai Allah Ya tambayeka dangane da kiwon da ya baka, adalcinka kadai zai iya cetonka a wannan lokaci..

..A wannan rana ba Vice President (VP), a wannan rana ba Sakataren gwamnati (SGF), a wannan rana ba Chief of staff (CoS), a wannan rana ba Chief security officer (CSO), a wannan rana ba babban dogarin shugaban  kasa (ADC), a wanann rana ba Convoy ba jami’an tsaro. inji Malam Kabiru Gombe

Ina baragurbin Musulmai da suke cin fuska wa su Malam Kabiru Gombe wai basa yiwa shugabanni nasiha saboda suna cikin gwamnati? da fatan zaku yiwa Malam adalci

Malam yayi nasiha a takaice mai girma da kuma fa’idah, nasihar ba wa shugaba Buhari kadai ba, duk wanda Allah Ya dauramasa nauyin shugabanci ko na gidansa ne to wannan nasihar ta shafeshi

Allah Ka sakawa Malam Kabiru Gombe sakamako da gidan Aljannah

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button