Labarai

Me Ya Sa Tun A Karon Farko Gwamna Yahaya Bello Na Jihar Kogi Ya Ki Yarda Da Cutar Corona Virus?

Advertisment

Gwamna Yahaya Bello ya bayyana cewa hukumar NCDC tana tallata cutar Corona Virus kuma tana lalata rayuwar mutane.

Ya ce “Rainin wayon Cutar ya isa haka! An samu sabbin masu dauke da cutar har mutum 386? Mun yi wauta sosai!

“Kuma an sallami mutane 679 da suka warke daga cutar. Me kuka ba wa waɗannan da suke dauke da cutar har suka warke?

“Covid-19 yaki ne, kuma a lokutan yaƙin za ka sa kowa ya shirya. Ku fadawa ‘yan Nijeriya abu daya da kuka yi ga wanda ya warke daga cutar, sannan ku fadi abinda za mu aminta game da abubuwan da za mu yi domin mu kubuta.

Advertisment

“Shin cutar Corona ta fi kashe mutane ne sama da cutar tarin fuka, ciwon huhu, ciwon daji?

“Mutane suna mutuwa a kowacce rana dalilin wasu cututtuka na wata rashin lafiya saboda tsoron zuwa asibitoci.

“Mutane suna da ciwon sukari, ciwon koda, ciwon hanta, cututtukan zuciya, cututtukan daji, hawan jini, HIV kanjamau, cutar sankarar hanji, da sauransu, wasu suna buƙatar zuwa wasu jihohin don samun damar zuwa wasu asibitoti. Da zarar sun mutu cikin rashin lafiyan sai kaga ana lissafa su cikin masu dauke da cutar corona.

“Me ya sa muke tallata Corona a Nijeriya?
Me ya sa muke cutar da kanmu da gangan?
Kirkirar tsoro, wahala da tashin hankali kan dan kasa babban laifi ne.

“Shin ko kun san yadda mutane ke fafutikar neman rayuwa a kasar nan? Shin kun san mafi yawan wahalar da kuke tilastawa mutane ta tallata Corona?

“Yanzu za mu tilasta mana bude iyakokinmu domin shigo da shinkafa, za a iya cin abinci da kuma sauran nau’ikan hanyoyin sake cin abinci ba tare da bata lokaci ba, a lokacin da muke kusan wadatar abinci. Hukumar NCDC ta Ishemu da wannan siyasar da take wasa da Rayukanmu.

“Wannan shine wata na biyu da muka rufe ofisoshinmu ba tare da wata hanyar rayuwa mai inganci ba, kuma kullum kuna kan kirga mana lambobin masu dauke da cutar kullum.

Shin kuna damuwa da yanayin da muka shiga na wannan rayuwar?

Da farko kun dauki kowane gidan Rediyo da Gidajen Television Gidajen Jaridu, don tallata Cutar Corona.

Kowane second biyu suna cikin tallata Corona, don kafa tsoro a cikin mutane yayin da kuka san wannan cutar ba hukuncin kisa take yi ba….

Shugaban kasa ya yi ta kokarin samun bunkasar tattalin arzikin kasar, kuma a cikin idanunsa, komai yaki yayi daidai, babu wata jiha da za ta yi alfahari da naira biliyan 1 na tattalin arziki a yanzu.

Hukumar NCDC ta dakatar da siyasantar da cutar Corona, ta dakatar da tashin hankali, da lalata tattalin arzikinmu” inji Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello.

Sources: Facebook/rariya

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button