Labarai

Wata sabuwa ! An fara shirya fim a sararin samaniya

Advertisment

FITACCEN jarumin finafinan Amerika ɗin nan, Tom Cruise, ya fara aiki kan wani fim da za a ɗauka a sararin samaniya (outer space), inji wata sanarwa daga Hukumar Ilmin Jiragen Sama da Kimiyyar Sararin Samaniya ta Ƙasar, wato ‘National Aeronautics and Space Administration’ (NASA).

Shugaban hukumar, Jim Bridenstine, shi ne ya bayyana haka a wani saƙo da ya tura a Twitter.

A cewar sa, “NASA na farin cikin yin aiki da @TomCruise kan wani fim da za a ɗauka a cikin (tashar bincike) @Space_Station!”

Ya ƙara da cewa,
“Mu na buƙatar kafafen yaɗa labarai da aka sani da su taimaka wajen saka wa sabbin injiniyoyi da malaman kimiyya shauƙin yin aiki don cimma manyan muradan @NASA.”

Mista Bridenstine bai bada cikakken bayani ba, to amma saƙon da ya tura ɗin ya biyo bayan wani rahoto ne da jaridar masana’antar finafinan Hollywood mai suna ‘Deadline’ ta wallafa ran Litinin inda ta ce Cruise ya fara aiki tare da kamfanin Tesla da ɗan kasuwar nan mamallakin kamfanin SpaceX, wato Elon Musk, domin shirya fim da zai kasance na farko a tarihi da aka ɗauke shi a sararin samaniya.

Fim ɗin, wanda na gumurzu ne, ba a yi nisa kan aikin shirya shi ba, a cewar ‘Deadline’.

Mujallar Fim ta ruwaito cewar wakilan jarumi Tom Cruise ba su amsa wa kamfanin dillancin labarai na Reuters buƙatar su ta faɗin wani abu kan wannan al’amarin ba.

Shi dai Thomas Cruise Mapother IV, wanda shi ne jarumin fitaccen fim ɗin nan na “Mission: Impossible”, ɗan shekara 57 ne.

Ya samu lambobin yabo da dama a kan aikin sa, ciki har da Kyautukan Golden Globes guda uku da zaɓen Kyautukan Academy guda uku.

An ƙiyasta cewa kuɗin da ya mallaka a yanzu sun kai dala miliyan 570, kuma ya na daga cikin jaruman fim da su ka fi kowa tsada a duniya.

Finafinan da ya fito a cikin su sun samu ribar sama da dala biliyan 4 a Arewacin Amurka, da ribar sama da dala biliyan 10.1 a sauran sassa na duniya.

Hakan ya sa ya na daga cikin jarumai da su ka fi kowa kawo riba a tarihin shirya finafinai a duniya baki ɗaya.

Tashar binciken sararin samaniya, wato International Space Station, inda za a ɗauki fim ɗin

An san shi wajen fitowa a finafinan gumurzu na ban-mamaki, kuma shi ne ya ke yin dukkan abubuwan saida rai da ake ganin sa a kai a duk finafinan sa.

Wannan akasin wasu jaruman ne da ke amfani da wasu gwarzayen wajen yin ayyukan kasada a finafinai a madadin su.

Misali, Cruise ya tuƙa jiragen sama na yaƙi da hannun sa a wani sabon fim da zai fito mai suna “Top Gun: Maverick,” sannan ya ɗafe a jikin jirgin sama lokacin da jirgin ya tashi a fim ɗin “Mission: Impossible Rogue Nation” a shekarar 2015, sannan ya hau kan benen nan da ya fi kowanne gini tsawo a duniya, wato Burj Khalifa da ke birnin Dubai a fim ɗin “Mission: Impossible Ghost Protocol.”

A watan Fabrairu aka tsaida ɗaukar fim ɗin “Mission: Impossible 7” a  lokacin da annobar cutar korona ta fantsama a ƙasar Italiya.

Daga bisani annobar ta sa an rufe dukkan masana’antar Hollywood da wuraren shirya diramomin talbijin da kuma gidajen sinima.

– Fassara daga rahoton Reuters da NAN

#Fimmagazine

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button