Addini
Bidiyo : Muhimmin Sako Daga Prof Mansur Sokoto
Advertisment
Wallahi ban taba ganin sakon da ya kwantar min da hankali, akan Codi-19 kamar na Professor Mansur Sokoto
Yaka mata al’ummar Nigeria su saurari wannan jawabi Wanda Sheikh ya sake a jiya da daddare, babu shakka jawabin ana bukatarsa a irin wannan yanayi da muke ciki, kuma babu shakka jawabin yayi ma’ana kuma yana kwantar wa al’umma hankali, tare da warware shubuhohin wasu malamai, da suka jefawa al’umma, akan abunda ya shafi sallar juma’a da umra da kuma khamsussalawat, akan wannan bala’i na Coronavirus.
Shehun malamin ya bada tarihin wata annuba data afkawa duniya, wadda ta kashe dubbai anan Nigeria, annubar kusan ta shiga duk wata jaha a Nigeria annubar wacce ta abku a shekara 1918-9 wacce ta shafe kusan shekara, ta kashe akalla mutum kusan dubu dari biyu a kasar Nigeria kawai. Hoton dake kusa da Video na alkaluman annubar ne! Wanda aka samu.
Babu shakka na yabawa Sheikh Allah ya kara maka fikra, a wannan jawabin ka kacire al’umma daga wannan duhu da aka fada ana dafe dafe, an kasa samun madafa.
Ni kusan karfe daya na kalli Video wallahi ji nayi kamar wata allura aka saka min wani irin dadi danaji wallahi.
Yaka mata ka saurara dan uwa. Kuma ka taimaka kayi Sharing na wannan Video wallahi zaka samu lada insha Allah. Domin duk Wanda ya saurara zai amfana dashi.
Muhammad Ismail Ali.
14-4-2020.
14-4-2020.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com