Addini

Kungiyar Izala Ta Raba Tallafin Naira Miliyan Talatin 30M Ga Marayu 6,800 a Abuja (Hotuna)

Kungiyar JamaátuI Izalatil Bid’ah WaIqamatis Sunnah, Jibwis Nigeria, reshen birnin tarayya Abuja ta raba tallafi da suka hada da abinci, tufafi, kudade da adadin su ya kai kimanin N30,186,760 ga marayu da gajiyayyu guda 6,800.

Shugaban Kungiyar natarayyar Nijeriya, Ash-sheikh Dr. Imam Abdullahi Bala Lau ne ya jagoranci rabon kayakin marayun wadanda aka tara su a majalisin tafsirin Ramadaan wanda sakataren kungiyar ta kasa, Ash-Sheikh Dr. Muhammadu Kabiru Haruna Gombe yake gabatarwa tare da alaramma Ahmad Ibrahim Suleiman a masallacin Umar Ibn Khaddab dake hedikwatar kungiyar JIBWIS dake birnin tarayya, Abuja.Kungiyar Izala Ta Raba Tallafin Naira Miliyan Talatin 30M Ga Marayu 6,800 a Abuja (Hotuna)

Da yake jawabi a wurin taron, shugaban Kwamitin marayu na Abuja, Alh. Abdullahi Abdulmalik Diggi ya bayyana cewa sun tallafa wa marayu da kayaki mabanbanta na jinkai. “A Jumlace mun taimaka wa marayu da gajiyayyu 6,800. Mun sayi shinkafa buhuna 530 akan kudi N14,167,00; mun sayi atamfa da shadda na kudi N2,382,800; zamu bayar da kudindinki N5,000 ga marayu guda 1000 wanda a jumlace kudin ya tashi N5,000,000 kazalika munyi sauran hidimu da ya kai N940,000. Daga cikin jumlar abun da aka samu, munyi amfani da N22,603,800. Ya zama muna da sauran N7,582, 960 saura a asusu.” Inji shugaban kwamitin na marayu.Kungiyar Izala Ta Raba Tallafin Naira Miliyan Talatin 30M Ga Marayu 6,800 a Abuja (Hotuna)

Da yake jawabi a wurin raba kayan tallafin marayun wanda ya guda a harabar masallacin Umar Bn Khaddab, Sheikh Muhammadu Kabiru Haruna Gombe yayi kira ga alumman musulmai da su kara kaimi wajen jinkan marayu. Shehin malamin ya bayyana cewa marayu suna kara yawa a kowani bangare, saboda haka dole a tashi tsaye wajen taimaka mu su. Shehin malamin yace ta wannan hanya kadai, Allah SWT zai tausayawa al’umma musamman a hali da ake ciki na rashin tsaro a Nijeriya.

Shima a nasa jawaban, Sheikh Bala Lau ya bayyana cewa aikin jinkan maraya aiki ne da zai kai mutum kololuwar matakin martaba a wurin Allah SWT. Ya kuma bayyana cewa akwai shiri na musamman don daukan nauyin karatun marayun tare da aurar da ‘yan mata daga cikin su. Shugaban ya kuma yi kira ga masu tafsiri a masallatai da su cigaba da dabbaka wannan aikin na taimaka wa marayu, ya kuma yi kira da a dage da rokon Allah SWT akan rashin tsaro da Nijeriya take fama da shi.

An mika kayayyakin ga marayu a wurin taron, inda daga yanzu harzuwa karshen Ramadan za su cigaba da karba, kamar yadda kwamitin ta bayyana.Kungiyar Izala Ta Raba Tallafin Naira Miliyan Talatin 30M Ga Marayu 6,800 a Abuja (Hotuna)

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button