Labarai

VIDEO: Kalli Bidiyon Maigirma Minista Yayi Kuka Da Zubar Da Hawaye

Advertisment

Allahu Akbar! Dazu a gurin walima da aka shirya wa Malam Isah Ali Pantami a Masallacin Annoor, bayan an bashi dama ya gabatar da jawabi, sai yace ba murna zaku tayani ba, akwai babban aiki da kalubale a gaban mu, da kuma amana da aka bamu.., kawai sai ya fashe da kuka, jawabin da bai karasa ba kenan
Wannan kalubale ne ga mahassada da suke cewa Malam yanzu kuka ya kare tunda ya zama minista, ko shekaran jiya ma sai da naga wani marar kunya yana fadin haka cewa Malam kuka ya kare.
Karfin imani da tausayi da tunanin lahira da tsoron Allah shi ke sa bawan Allah musulmi yayi kuka, mu a garemu wannan rahama ce.
Wannan shine karon farko a tarihin Nigeria da wani Minista ya zubar da hawaye saboda tsoron Allah akan girman amana da aka bashi
Yaa Allah Ka yi riko da hannun Malam, Ka masa jagoranci, Ka bashi nasaran sauke amanar da aka daura masa Amin
Ga bidiyon nan Kasa

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button