Labarai

Ango Ya Saki Matarsa Bayan Daya Gano Ba A Budurwa Ya Aureta Ba

Wani angon watanni 4 da aka nemi mu sakaya sunansa, ya saki amaryar daya aura tare da neman ta maida masa da sadakinsa bayan daya gano ta masa karyar budurci.

Yace kamin aurenta ta tabbatar masa ita budurwar ce gal a leda, amma sai ya samu akasin hakan bayan daya jaraba.

Majiyar mu yace angon bai saketa ba har sai bayan da suka yi watanni 4 da auren nasu. Inda yace shima bai san dalilin daya sa sakin ya dauki tsawon lokaci ba kamin a yi.

Da wakilinmu ya nemi jin ko an maida masa sadakin nasa, yace idan ya samu karin bayani zai tuntubemu.

Shi dai wannan angon da alamu dai ba saurayi shima yake ba. Duba da yadda ya iya gano macen da ba budurwa take ba duk kuwa da hikimar da mata suke yi na matsai gabansu ya dawo kamar na jarirai.

Madogara :A Tonga

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button