Labarai

Gaskiyar Abin Da Sheikh Dr. Isa Ali Pantami Ya Fada

Daga Anas Saminu Ja’en

Sheikh Dr. Isa Ali Pantami Malam yana magana ne akan yin imani ga Allah Ta’ala kuma ya yi wannan bayani ne a lokacin da yake gudanar da Tafsir a ranar 4 ga watan Ramadan a masallacin Annoor Masjeed Wuse ll a Abuja, Malam ya ce hakikanin nagarta shi ne “Man’ama Billahi” wanda yai imani da Allah Ta’ala  duk abun da yake daga wajan Allah ka gasgatashi kar ka tsaya kana tinanin ya yi ko bai yi ba.

1- ka yi imani cewa Allah Ta’ala akwai shi.

2- Allah shi ya halitta shi ya mallaka kuma shi yake jijjuyawa.

3- Shi kadai ya dace a bautawa.

4- kai imani da sunayen sa da siffofin sa, ilimin Allah ya fi karfin hankalin ka ya fi karfin hankali na.

Malam ya ce duk abun da Allah ya yi ka yadda akwai hikima a ciki wannan jahilci ne wasu lokacin hatta ga masu mulki ina tuna shekaru kamar bakwai 7 da suka wuce a arewacin kasar nan daga cikin mafi fuskoki da tasiri, akwai wanda ya sha giyar mulki ya ce shi ya rasa me yasa Allah ya halacci Sauro ne.

Har Malam yake cewa wai shi a matsayin sa ba Injiniya ya gama tinanin sa bai sai me yasa Allah ya yi wannan ba, yanzu akwai imani a wannan wajan mutum ya ce wai bai san me yasa Allah ya yi wata halitta ba a cikin halittu wai ya gama tinani, saboda wani lokacin jahilci ba abun da baya sawa. akwai mai mulkin da ya tsaya ya ce Annabi S.W.T akwai wanda ya tsaya ya ce Allah S.A.W  akwai wanda ya ce zamanin Annabi Buhari in ba haka ba a ce mutum yana shugabantar al’ummar musulmai ya na Challenging kudira da ikon Allah Ta’ala inda addini da sanin addini wannan ma ai ba mutane bane, wannan bai da ce ko wankin bandakin masallaci a basu ba indai da ilimi ake abu But haka aka tsinci kai a ciki Allah Ta’ala ya karemu daga jahilci Allah ya kare mu daga jahilai da kuma aikin jahilci

Wannan shi ne abun da Malam ya fada Allah ya sakamasa da mafificin alkairi, duk wanda mai yi imani da Allah ba shi ne zai ja da ikon Allah da abun da Allah Ta’ala ya halitta duk musulmin kwarai yasan haka.

Amman saboda kin Allah da siyasar jahilci ta wannan zamani da wasu ke yi suna ta yada cewar Dr. Isa Ali Pantami wai ya zagi Kwankwaso kaf a karatun babu inda ya kama sunan kwankwaso ballantana ya zage sh, idan kuma akwai wanda ya ji ya anbaci sunan sai ya sanar da mu musamman yaran kwankwaso wadanda ba bu mutum mai daraja da kima a idanun su kaf fadin duniya kowa suka ga dama sai su zage shi su ci mutuncin sa wannan kuskure ne babba a rayuwa wallahi, idan kuma shi kwankwaso shi ne ya yi wancan furucin na cewar bai sai me yasa Allah ya yi Sauro ba sai ku fada mana? A cikin masu zagi da cin mutuncin Malam idan kuma akwai wanda yake da ja akan hakan? To ya taimaka ya kawo mana Video ko Audio, dan Allah mu daina yada jita-jita domin ni a yanzu haka ina da shi kuma duk wanda ya kawo wallahi wallahi wallahi akwai kyata mai tsoka.

Source:hausatimes

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button