Labarai

Kotu ta yanke wa dilan wiwi hukuncin shekara 10 a gidan yari

Wata babbar kotun tarayya da ke Kano mai lamba 3 ta yanke hukuncin daurin shekaru 10 a gidan kaso ga wani mutum Muhammad Bako Sambo, mai safarar tabar wiwi.

Daily Nigerian Hausa na ruwaito Sambo na daga cikin masu safarar miyagun kwayoyi guda bakwai da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta kama ta kuma gurfanar a gaban mai shari’a S.A Amobeda a watan Oktoba.

A cewar jami’in hulda da jama’a na hukumar NDLEA, Sadiq Muhammad Maigatari, an yankewa Sambo hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari.

“Sambo, wanda aikin sa ya hada da safarar tabar wiwi mai yawa daga Ondo da sauran jihohin Kudu zuwa Arewa, an kama shi ne a ranar 11 ga Nuwamba, 2020.

Jami’an NDLEA da ke sintiri a kan hanyar Kano zuwa Zariya ne su ka nuna shakku inda suka dakatar da wata motar Honda wadda da farko ta ki tsayawa.

Ya kara da cewa bayan an kama wanda ake zargin ne a unguwar Hotoro a jihar Kano, sai aka fara gudanar da bincike a shelkwatar hukumar.

Binciken a cewar Maigatari, binciken ya kai ga gano busasshen ganye da ya kai kilogiram 201 da ake kyautata zaton na tabar win ne, inda ya kara da cewa an kuma gano cewa mazaunin ne Lokogoma ne a Abuja.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button