Uncategorized

LASTEST:Hukumar SSS zata kama Alkalin kotun koli, da wasu bakwai

Duk da kace nace da samamen da jami’an hukumar tsaron sirri ta kai gidajen wasu manyan alkalan kasar nan ya janyo, rahotanni na nuna hukumar zata kai samame kan wasu manyan alkalai nan bada dudes a ba, inji rahoton jaridar Premium Times.

Jaridar ta samu labarin ne daga wani jami’in hukumar daya bukaci a sakaya sunansa wanda ya tabbatar mata da cewa akwai sauran mutane takwas da suka rage ma hukumar ta kama, daya daga cikinsu alkalin kotun koli ne. majiyar ta bayyana cewa mutane 8 din da za’a kamo na daga cikin alkalai 15 da hukumar ke gudanar da bincike a kan su kan zargin aikata almundahana. A karshen makon daya gabata ne dai aka cafke 7 daga cikinsu, inda ake sa ran kama sauran mutane 8 nan bada dadewa ba.
Jaridar Premium Times ta ruwaito a yanzu haka alkalai 7 da aka kama suna daure a ofishin hukumar tsaron sirri na SSS, alkalan kuwa sune: mai shari’a Inyang Okoro da mai shari’a Sylvester Ngwuta dukkansu na kotun koli; mai shari’a Adeniyi Ademola na babban kotun tarayya, Abuja; mai shari’a Kabir Auta na babban kotun jihar Kano; mai shari’a Muazu Pindiga na babban kotun jihar Gombe, mai shari’a Mohammed Tsamiya na kotun daukaka karat a garin Ilori, sai babban mai shari’a na jihar Enugu I. A. Umezulike.
Jaridar ta ruwaito majiyar tata tana cewa, banda ma alkalan, akwai wasu ma’aikatan kotun su uku da aka gayyata don amsa tambayoyi. Sai dai hukumar ta kyale iyalan alkalan dasu ziyarci alkalan.
A wani hannun kuma, tun bayan samamen da hukumar SSS ta kaddamar a gidajen alkalan nan a daren ranar asabar 8 ga watan Oktoba, yan Najeriya da dama sun bayyana damuwarsu game da yima doka biyayya a gwamnatin Shugaba Buhari.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button