Uncategorized

Abinda Namiji Ke so Ga Mace

Ita dai mu’amala wata aba ce da ake so mutum ya kyautata ta, tsakanin sa da kowa,har wanda ba musulmi ba. Ya kamata mata su lura da wadannan halayen:
Biyayya
Dole ne a matsayin ki na matar aure ki kasance mai biyayya a cikin duk abin da mijin ki ya ce kiyi, in har bai sabawa abin da Allah yake so ba. Ki ji a ran ki ke fa bautar Allah kika zo, kuma ki sa a ranki cewa aure hanya ce da zaki nemi Aljanna da ita.

Gaskiya:
Fadin gaskiya a kowanne lokaci yana da muhimmanci kuma zai jawo miki kauna da soyayyar mai gidan ki. Haka kuma zai jawo miki yardar Allah. Manzon Allah (SAW) ya ce: “…….lallai ita gaskiya tana shiryar wa zuwa ga biyayya ga Allah, ita kuma biyayyar Allah tana shiryar wa zuwa Aljanna……….Ita kuma karya tana shiryarwa zuwa fajirci, shi kuma farirci yana shiryar wa zuwa wuta……..”.
Ashe dai fadin gaskiya zai iya jawo yardar Allah, domin kuwa in har an shiga Aljannah ai babu sauran fushin Allah kuma; kamar yadda karya zata iya dawo fushin Allah.

Rikon amana:
Ki kasance mai rikon amanar mijin ki. Ki kiyaye kan ki daga duk wani namiji wanda zai iya sa mijin ki ya zarge ki a kan sa. Ki yanke alaka da duk wanda mijin ki baya son kiyi alaka da shi, kuma kar ki kulla wata alaka da duk wanda mijin ki baya so kiyi alaka da shi. Ki kula da dukiyar sa, abin da ya shafi kayan amfani na gida ko kadarar sa ko kuma kudin sa. Ina jin labarin ana cewa wasu mata har duba aljihun mazajen su suke yi ko zasu samu kudi su dauka! Yar uwa ta kar ki yi haka domin rana dubu ta barawo, rana daya ta mai kaya.
Kunya
Dole ne mace ta kasance mai kunya. Dole ne duk abin da zai sa mijin ta ya ji kunya a gaban jama’a ta kiyaye shi.

Hakuri
Yar uwa ta kada kiyi tunanin rabin ran ki ba zai bata miki rai ba. Wasu matan idon su yana rufewa, wai don ita kadai ce ‘ya mace a gidan su ko ita ce ‘yar auta ko ita kadai aka haifa a gidan su, don haka yanda ake shagwaba ta a gidan su haka za’a yi mata a gidan miji. Eh! Hakan zai iya faruwa, in kin yi sa’ar mijin da yake da fahimta. Zaki iya samun wanda zai baki gatan ma da ya fi wanda kika samu a gidan ku, amma fa ki sa a ranki wata rana dole a samu matsala. To duk lokacin da matsalar nan ta faru kiyi hakuri ki manta da zancen. Wannan shi zai kara miki zaman lfy a gidan mijinki.

Iya magana
Wasu matan basu iya magana ba. Suna ganin sa’annin su ne koda kuwa mijin ya fi ta da shekara goma. Hajiya ki fahimci cewa shi fa namiji kan sa a dan kunbure yake. Ko da kuwa kin girme shi da shekaru, shi yana ganin shine a gaba, domin shi ne mai gida kuma a ko da wanne lokaci yana da ikon da zai yi abin da ya ga dama a gidan sa. Sai kaga miji yana bawa mace labarin wani abu mai muhimmanci, sai tace “tsaya, kace Allah”! wannan zai sa ya ga kin raina masa hankali har ya fara tsanar ki.
Sauraro mai kyau
Wasu matan idon miji yana yi musu zance sai kaji sun ci gaba da harkokin gaban su. Idon yayi magana sai tace “to ba kunne ne yake ji ba? Ai ina ji ka fada mana”. Wasu kuma miji yana yi musu magana sai kaji suna cewa “kai ni ka dame ni”. To gaskiya hakan zai iya jawo miki matsala. Ba lallai sai ya sake ki ba, zai iya canja yanayin mu’amalar sa da ke kuma hakan zai hana ki kwanciyar hankali a gidan miji.

Godiya
Godiya a duk lokacin da miji yayi miki wani abu komai kankantar sa yana da muhimmanci kuma yana kara soyayya. Ki tuna fa Allah ma yana so ayi masa godiya kamar yadda yace “……tabbas in kuka gode min zan kara muku, (amma) kuma in kuka kafirce min, to azaba ta mai tsanani ce”.
Haka zalika, godewa miji zai sa ya kara miki wani abun ma da baki yi tunani ba. In yayi miki abu kika gode, sai ya samu kwarin gwiwar yi miki wani abu, amma in baki gode ba ko kika raina abin da ya kawo miki, to nan gaba ko yayi tunanin yi miki wata kyauta sai ya fasa saboda yana tunanin kar ya kawo miki, ki watsa matsa kasa a ido.

Neman shawarar mijin ta
Neman shawarar mai gida abu ne mai kyau. Hausawa sun ce “ana yi da kai yafi ace ba’a yi da kai”. Neman shawarar mai gidan ki idon zaki yi wani abu zai saka shi yaji ashe kin dauke shi da muhimmanci kuma zai yi kokarin ya baki shawara mai kyau, dai-dai gwargwado.
Rashin yawan kuka
Wasu matan suna da yawan mita. Duk abin da aka yi mata sai tayi magana. Wannan ya hada da in mai gidan ne yayi mata laifi ko wani ne daga dangin sa. Hakan yana da illa, domin yana daya daga cikin dalilan da suka sa mata suka fi yawa a wuta a lahira, saboda hadisi ya tabbata cewa wata ranar sallar idi Manzon Allah (SAW) ya yi sallar idi sai yayi huduba bayan sallar, sannan ya wuce yayi wa mata wa’azi, a ciki yake cewa “ku yawaita sadaka, domin kune mafi yawan makamashin wuta”. Sai wata mata ta tashi tsaye tace saboda me, ya Manzon Allah? Sai yace: “kun kasance kuna da yawan kai kara, kuma kuma butulce wa abokin zama (wato miji)”.
Ashe kenan wadannan abubuan guda biyu zasu iya kai wa mace wuta. Don haka yar uwa, ina baki shawara da ki zama mai godiya ga mijin ki kuma ki daina yawan magana akan kowanne karamin abu da bai kai ya kawo ba.

Taimakon sa in Allah ya baki dukiya
Wani lokaci zaka ga mace ta fi mijin ta karfin samu. To a wannan lokacin ya kamata ta rinka rage masa wasu abubuwan na gida. Hajiya, zaki iya yi wa mai gida dinki bai sani ba, sai dai kawai ya ga an kawo masa kaya a dinke, ko kuma ki dauki nauyin wani abu a gida, ki bada kudi a yi. In dukiyar taki ma ta kai matsayin da zaki bada zakka kuma kin san mijin ki ya cancata, zaki iya fitar wa ki bashi, domin shi yake da hakkin ciyar da ke ba ke kike da hakkin ciyar da shi ba, kamar yadda matar Abdullahi Ibn Mas’ud tayi.
Alaka da sauran mutanen da suka shafi miji:
wadannan sun hada da iyayen miji, abokiyar zama, kannen miji da yayun sa, ‘ya’yan miji, wadanda ba ita ta haife su ba da ‘ya’yan da ta haifa. Ya zama dole mace ta kula da wadannan mutanen gaba daya, kuma ta mutunta kowa a cikin su.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.comMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button