Darajar Mijinki Kula Dashi Amarya (karanta)
Wannan kuwa ya zama dole iyaye mata su ladabtar da ‘ya’yan su tun kafin ayi musu aure, su koya musu kowanne irin aikin gida musamman girki. Ki kasance kin iya girki kala-kala kuma mai dadi wanda zai sa mijin ki santi har ya manta da wani bacin rai da ya same shi ma a waje, ko kuma ta bangaren ki.
Ya zama dole mace ta yarda mijin ta shi ne shugaba a kan ta, ko da kuwa ta girme shi da shekaru, ko ta fi shi kudi, ko ilimi, ko matsayi, ko karfi kodai wani abu na rayuwa. Ki tuna fa shi ne ya je har gidan ku ya nuna sha’awar kasancewa tare da ke na tsawo wani lokaci da bashi da karshe sai fa in mutuwa ta zo. Shi ne yake da hakkin kula da ke dangane da ci, sha, tufafi, matsugunni (wato gidan da kuke zaune) da kuma biya miki bukatar da babu wanda ya isa ya biya miki banda shi (wato . Allah ya fada a cikin littafin sa “maza sune Hanyoyin girmama mai gida suna da yawa. Sun hada da:
Boye sunan mai gida: wasu matan kawai sai ka ji suna kiran mai gida da sunan sa kai tsaye. Gaskiya yar uwa in kina so ki samu karin matsayi a wurin mai gidan ki dole ne ki boye sunan sa. Zaki iya cewa mai gida, baban wane/wance, doctor in likita ne, engineer in engineer ne, honourable, darling, sweetheart, sweety, bestie, nawan, the one, my heart, my love, k’ok’on zuciya ta da sauran su.
Yin kasa da sauti in kina magana da shi: mace ta gari itace wacce bata daga muryar ta idon tana magana da mijin ta, ko da kuwa ran ta ya baci. Yin hakan zai iya fusata shi kuma ta yiwu ma har yayi abin da bai kamata ba. Idon kika fahimci cewa ya hau sama, ran sa ya baci, sai ke kuma ki sauko, kuma ki yi masa magana mai dadi.
Bashi hakuri in kin yi laifi: dole ne mace in tayi laifi ta bada hakuri. Wasu matan in sun yi laifin ma aka fada musu sai su fara musu, suna kokarin kare kan su. Mace ta gari ita ce wacce in tayi laifi zata yarda tayi kuma ta bada hakuri tare da cewa inshaallahu ba zata sake yin irin haka ba. Yar uwa ta, abin da ya fi miki kyau ma shi ne ke ya kamata ki fara sanar da mijin naki laifin ki, sannan ki bada hakuri. Wasu mazajen in suka ga abu na laifi da fada zasu fara. Amma in ke kika fara sanar da shi sannan kika bashi hakuri, to inshaallahu komai zai zo da sauki
Daukar shawarar sa: idon mijin ki ya baki
shawara akan wani abu ya kamata ki girmama ra’ayin sa in har bai ci karo da addinin Musulunci ba. Wannan shi zai tabbatar masa da cewa kina girmama shi.