Uncategorized

BABI NA DAYA : SAWUN BARAWO !

NWA®
SAWUN ‘BARAWO
(1)
Bismillahirrahmanirrahim.
***
Da fiiito ya shigo gidan kamar kullum, haka nan kuma ba tare da ya dubi kowa dake falon ba yanemi matsugunni a gefen kakar su yazauna, kasancewar ta halitta d’aya dake k’aunar shi a duk fad’in gidan nasu.
“Kukus ya akayi neh”? Naga fuskar ki a da’kuneh”? Ya jere mata tambayoyin sakamakon ganin yanda tai jigum takasa koda shafo kan shine kamar yanda ta saba matuqar suna zaune guri guda.
Ganin takasa koda kallon shi neh yasaka shi watsa idanuwan shi ga sauran halittun dake zaune a k’aton falon gidan nasu. Tab’e bakin shi yayi cike da halin ko in kula bisa alamun tashin hankali daya fuskanta daga dukkanin rayuwakan dake zaune a falon.
Ganin atmosphere (yanayin) da gidan ke ciki yasaka shi mik’ewa da niyyar komawa inda ya fito, ba tare da yak’ara kallon kowa ba yamik’e da niyyar ficewa daga falon.
“Mara mutunci ina kake tunanin tafiya”? Ya tsinkayo muryar mahaifiyar shi na fadi cike da masifa. Batare da ya kula da maganar ta ta ba yak’ara sauri domin ganin ya fice daga gidan baki d’aya.
“Wallahi safwan idan ka k’ara koda taku d’aya neh daga inda kake ban yafe maka ba! ” Chak ya tsaya yana mai yin kicin-kicin da ragowar sassaucin dake shimfide bisa fuskar shi.
Juyowa yayi yadawo cikin falon yai masu tsaye k’erere, haka nan kuma ya rik’a bin ragowar yaran gidan da harara tamkar su suka hana shi barin gidan.
Babban yayan su kabir shi neh yai k’undumbalar yi mashi nuni da yasami guri ya zauna, ba yayi musu k’erere ba a kah.
“Malam ban son shishshigi ka kama kanka”! Amsar daya bashi kenan yad’auke kan shi daga kan sa ya maida kan hajiyar su dake zaune tana bin shi da kallon kaji haushi.
“Nifa ina da abinyi” ya wurga maganar ga koma wa Allah yabaiwa damar ji. Duk da ba kallon hajiyar tasu ya yi ba yayin da yake furta maganar amma hakika kowa yasan da ita yake.
Sauke nunfashi hajiyar tayi gamida girgiza kai cike da godewa Allah (S. W. T) bisa irin kangararren yaro da ya bata.
“Idan baka dibi daraja ta ba na mahaifiyar da ta kawo ka duniya ba, inaso kadibi girman Allah’n daya hallicceka kazauna ina son yin magana da kai”. Mahaifiyar tasu ta fadi maganar tana mai kallon jajayen k’wayar idanun tilon d’an nata daya fice zakka a dukkan ‘ya’ya takwas da Allah ya albarkace su da su.
“Ai kin gama magana hajiya tunda kika taimaki kan ki kika ha’da ni da mai dukah! ” Ya ida maganar yayin da yake sake samun matsugunni kusa da kakar ta su a karo na biyu.
Shiru falon yasake d’auka, hakan yasa shi jin sheshek’ar kuka dake tashi a hankali ta side(gefen) daya hangi fitsararriyar yarinyar da hajiya kan iya b’atawa da kowa a kan ta, duk kuwa da cewa ba ita ta kawo ta duniya ba.
Harara ya bita da shi, wanda ba lallai bae ta gani diba da yanayin tashin hankalin da take ciki, hakan yasa yaja wani mugun tsaki cike da jin sabon haushin yarinyar nasake lullube zuciyar shi.
“Mama na d’ago kan ki ki dube ni, ki kuma nutsu ki gaya mani tsakanin ki da Allah a karo na ashirin, wani maras tsoron Allah’n neh yayi maki fyad’e a jiya da daddare? “
Tab’e baki yayi cike da jin sabon bacin rai na ziyartar shi, dama akan issue d’in su neh suka saka shi b’ata lokacin su yana sauraren su? Take ya yanke Cewar matuk’ar suka gama soki burutsun zancen su tabbas yazama dole ya bige masu warning na cewar kar asake yi masa irin haka, shi ina ruwan shi da shirgin su neh wai ma?

Yai k’wafa yana mai jin tamkar yatashi ya wawwanka wa kowane mahaluk’i dake zaune a falon mari. “Aikin banza yarinya taje tayo iskancin ta za’a wani zo a tara su ana zancen k’arya da borin kunya” ya saki pito gamida k’ara bajewa bisa kujerar daya ke cike da fatan suyi su gama zancen banzan su yak’ara gaba, dokin kuwa yana matuk’ar buk’atar sigarin sa.
Shiru tayi tana tuna irin hukuncin da zata iya fuskanta matuk’ar ta ambaci sunan wanda ya yaga mata rigar mutuncin nata a daren na jiya. Tuno da irin azabar da ya d’an d’ana mata yasaka ta bude bakin ta cike da sabon kukan daya sark’e mata mak’oshi tace “Mammy yaa saf… Safwan neh” ta ida maganar gami da rushewa da wani sabon kukan bak’in ciki.
Inba kunnuwan sa bane suke masa k’arya, tabbas yaji kamar yarinyar ta ambaci suna makamancin nashi, amma duk da hakan sai ya b’agarar da abinda yajin yana mai tunanin k’ila anyi wani bak’on safwan dinne a gidan na su batare da ya sani ba.
Gaba daya falon shi suka zubowa idanuwa suna masu Allah wadarai da shi a zuciyoyin su, domin kuwa sai dai a zuciyoyin na su suke da ikon tsine mai badai a gaban idanun shi ba, sanin rashin mutuncin shi da kowane mahaluk’i na gidan nasu yayi, kai har ma da mutanen unguwa baki d’aya.
Idanu cike da hawaye da kuma zallar b’acin rai hajiyar tasu ta fuskance shi cike da kakkausar murya. “Safwan”! Ta kirayi sunan nashi a karo na farko cikin wani irin b’acin rai da shi kan shi bai ta’ba ganin ta da shi ba.
Dago kanshi yayi cike da mamakin abinda keh shirin faruwa da shi a gidan. Hak’ik’a bashi da masaniya akan randa ya fara wasa da “Ramla” da har zati masa irin wannan wasan, amma yanzu zaiyi maganin abin.
Batare da b’ata lokaci ba ya sanya k’afafun shi biyu ya fizgota tsakiyar falon, haka nan kuma bai jirayi komi ba ya daga tafka tafkan hannuwan shi ya kwasheta d mari, ko kafin ta dawo hayyacin ta ya kuma kafsa mataa wani, a inda take tasakk wani marayan kuka cike da azaba “wannan shine a dake ka a hanaka kuka”
“Don ubanki ni sa’an wasan ki neh?” ya furta maganar yana huci gami da nunata da yatsan shi, wanda kafin ya rufe baki sai jin saukar nashi marin yayi a bisa fuskar shi data gama rufewa da b’acin rai.
Sanin mutum guda neh kad’ai zai ke iya masa Marin da akai mashi yasaka ko kallon wacce tai marin baiyi ba, illa sulalewa k’asa dayayi yariqe k’afafun kakar ta su data kasa cewa uffan tun zaman su a falon, duk kuwa da tsabagen masifa irin ta ta musammam inka tab’o shalelen ta safwan.
“Ban taba dana sanin zama sanadiyar zuwan ka duniya ba irin yau safwan!, ban tab’a jin makamancin b’acin rai ba kwatankwacin wanda kasa kani a yau safwan!…. Haka zalika ban tab’a sanin iskancin naka bai tsaya ga bare ‘yan waje kadai ba har da ‘yan uwanka! Kaico da mugun hali irin naka safwan… Kaicon ka! “
Ta numfasa cike da zallar bacin rai mabayyani a bisa fuskar ta, hakan yasa ko wane mahaluk’i dake falon ya sunkuyar da kan shi gamida yin Allah wadai da halin safwan d’in. Duk da dama an riga da ansan halin shi na kasancewa mutumin banza a duk ilahirin gidan, duk kuwa da kasantuwar shi d’a na uku a gidan na marigayi Alh. Mainasara.
Shi din yakasan ce fidda zakka a dukkan ilahirin gidan, domin kuwa a iya tarihin na unguwar tasu ba’a taba samun tantirin dan duniya ba irin safwan mainasara, tun yana k’ank’anin shi ya addabi jama’ar unguwa, har ma da abokan karatun shi na boko da islamiyya, domin kuwa duk wani yaro da babba dake zaune a unguwar tasu yasan safwan damisa! Sunan yasamo asali neh tun zamanin yana yaro, sakamakon rashin kirkin shi wanda duk yanda kuka kai ga yin shiri matuk’ar ka shiga gonar shi ko kayi mashi ba daidai ba, toh tabbas zai aje sanayya a gefe neh yaci uban da ya haife ka batare da shayin komi ba, ko waye kai kuwa.
Da k’yar da ya Allahu aka samu yagama secondary school, ita d’inma sai da ya maimaita aji shiddan fiye da sau uku sakamakon repeating d’in da hukumar makaranta ke masa a duk k’arshen zangon karatu.. Jami’ah kuwa sai da mabi autan gidan su yayi graduation, domin kuwa ka kaf sai da ‘kannen sa uku suka dade da had’a masters din su kafin aka samu ya hada degree, wacce ita din ma cuwa cuwa akasamu akayi masa ya fita da lower credit ta hanyar mijin yayar su dake rik’e da muk’a
min H.O.D a department din nasu na accounting.
Gama makarantar tashi bata saka shi nutsuwar nema wa kanshi abin yi ba, diba da yanayin girma da ya fara kama shi, mussamman diba da k’annen sa biyu maza masu bin shi har sun kawo matan aure an sha biki. Mutumin ku ko ajikin sa, sai ma bude sabon shafin iskanci da yayi mai lasisi, domin kuwa mussamman yayi k’aura daga gidan mahaifin nasu ya koma kwana hotel haka kurum don tsabar b’arnar kudi, acewar shi mahaifiyar su na saka mashi na mujiya bisa daren da yake yowa inya gama watsewar shi a club.
Atak’aicen tak’aitawa safwan mainasara tantirin dan iska neh na gidan gaba, domin kuwa babu salon iskancin da bayayi, hana k’arya dai baya shaye shaye duk iya shegen nashi a sigari kadai ya tsaya, daga ita kuwa koh wiwi bai k’ara ba akai.Bar shi dai da holewa da mata! Domin kuwa tantirin manemin mata neh, yanda yake chanza riga a kullum haka yake canza watsatstsun mata, wanda ko shi din bai neme su ba toh su kamda gudu suke kawo kansu, diba da kyakkyawar sura da Allah ubangiji ya hore masa.
Tabbas shi din kyakkyawa neh ajin farko, idan nace kyakkyawa ina nufin asalin kyawu da mai karatu zai iya k’imastaawa iyakar iyawar shi. Sai dai wani abu d’aya da ake shedar shi da shi shine kyauta! Kwata kwata bashi da rowa ko misk’ala zarratin, domin kuwa zai iya kyauta da abinda ke aljihun sa dukka koda kuwa last card din shi neh, hakan yasa talakwan unguwar su dama wadanda bana unguwar ba keh matuk’ar alfahari da shi gami da yi masa fatan shiriya a zuciyoyin su ako da yaushe.
***
A fusace yad’ago kan shi bisa jin furucin karshe da hajiyar tasu tayi, wanda hakan yasaka shi mik’ewa yana mai wani irin huci tamkar kumurcin maciji, atare da b’ata lokaci ba katse hajiyar tasu dake kan maganar ta yace…… “Kinsan Allah hajiya kodawa kike yawo bazan auri sauran wani k’ato bah” gara ki canza plan, domin kuwa wannan plan din naku baiyi tasiri ba akaina.”
” Safwan ni kake gayawa maganganu haka kamar tsarar ka…. Ni safwan? Toh bari kaji idan har ni na haifeka wallahi baka da mata sai ramlah! Idan har banda wannan k’addarar da ta riga fata kana tunanin nutsattssiyar yarinya irin ramlah ta dace da mutumin banza neh irin ka? Kai dai da kayi aika aikar yaga mata rigar mutunci kai kuma zaka d’inke ta, domin kuwa indai ina numfashi a doron k’asa baka da mata sai ramla shashasha maras tunani”
“Nadai gaya maku, idan na auri sauran ‘katon banza shege nake”! Daga haka yasaka k’afa ya shure ramlan dake gefe tana kuka a hankali ya wuce fuuu kamar kububuwa.
***
Ku dakace ni anan.
Toh ya kuka samu farkon labarin? Ina fatan yana k’ayatar da mai karatu? Ko dayake yanzu muka saka k’afa, fatana ku kasan ce da ni don ganin mun cimma manufa.
And your votes and comments do matters alot.
Love you loadz. ❤
Noorieyyaah. (Noor )

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button