Labarai
Wata Sabuwa : An Haifi Yaro Jariri Da Carbi A Jahar Gombe
Advertisment
Daga Fatima Ibrahim Mukhtar
A can baya an samu matar da ta haifi jariri da carbi a wuya a jahar Bauchi. Kwatsam a satin da mu ke cikin nan SARAUNIYA ta samu labarin wata mata mai suna Aishatu a unguwar Kagarawal a jahar Gombe ta haifi jariri rataye da carbi a wuya a asibitin gwamnatin jahar (specialist hospital).
Mahaifiyar jaririn ta shaida wa SARAUNIYA yaron ya haura watanni sha biyar kafin a haifeshi. An kuma haifeshi makale da carbi a wuya.
Iyalen gaba daya sun bayyana wannan karuwa a matsayin wata falala da Allah ya saukar wa zuri’arsu. Yaro da mahaifiyarshi suna cikin koshin lafiya.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)






