Buhari fa bai bude boda ba, kada ma ka bude babu abunda Buhari Ya Bude Sai Yaudara!
Masoya baba buhari dai suna dariya tare da tsalle wai gwanin su ya bude boda, basu San yaudarar su akayi da kalmar budewa, domin a dan basu kofa ta kariya ga gwamnati.
Sai dai Mista Joseph Attah kakakin hukumar kwastam ta Najeriya ya shaida wa BBC cewa dokar hana shigo da wasu kayayyaki da suka ƙunshi har da na abinci tana nan ba ta kau ba.
1.An hana shigo da shinkafa da taliya da man girki
2.An hana shigo da kajin Turawa ko talo-talo da ƙwai da nama
3.An hana shigo da sukari
4.An hana shigo da tumaturin gwangwani
5.An hana shigo da suminti
6.An hana shigo da sabulun wanka da na wanki da omo
7.An hana shigo da lemon kwali ko na kwalba da ruwan roba (amma bai shafi masu ƙara kuzari ba irin Power Horse)
8.An hana shigo da magunguna da suka ƙunshi Paracetamol da Aspirin da sauransu
9.An hana shigo da maganin sauro
10.An hana shigo da katin waya (recharge card)
11.An hana shigo da dardumar ɗaki
12.An hana shigo da iya kwandishan (Ac) da aka yi amfani da shi da kuma firji
13.An hana shigo da motoci da aka ƙera fiye da shekara 15.
Wadan nan kadan kenan daga abunda har yanzu bazasu saka kafa a Nigeria ba.
Shin dan Allah wani irin gaba ne ke tsakanin shugaban kasa da shinkafa?
Idan wadan nan kayayyakin nan basa shigowa dan Allah fada min ta ina aka bude boda?
Muhammad Ismail Ali.