Uncategorized

Tsaraba Ga Magidanta Kan Biyan Hakkin Aure

Dangane da yawan tes da wayoyi da muke yawan samu wasu mata ne suke kawo kukan rashin dadewan mazajensu a shimfida wasu kuma mazan ne ke kukan rashin kuzarin su, to in dai ana so a kiyaye sai an hakura da cin wasu ababen. A saboda haka ne ma dukkan bangarorin da ke da hannu wajen ganin an samu lafiyayyiyar dangantakar zaman aure mai gamsarwa ke kokari iya kokari wajen ganin daga bangarensu ba a samu matsala ba.

Mijin zai yi kokarinsa wajen ganin ya tsira da mutunci, girma da darajarsa wajen ganin bai tauye matarsa ba a wannan bangare, haka ita ma matar za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin cewa ta gamsar da maigida a duk lokacin da aka zo tarawa Wannan kokari da musamman maza ke yi shi ke sanya su a lokuta da dama shaye-shaye abinda suke kira da maganin karfin maza.

Wannan kuwa na iya zama na turanci (Biagra) ko na Hausa, irin wadanda za ka ji masu tallan magani a kan tituna da kasuwanni na kwarmata tasiri da ingancinsu Sai dai kuma, wadannan magunguna na karfin maza na da matukar illa na kai tsaye ko dai a nan gaba ko kuma a nan take. Misali, maganin karfin maza na turanci na bayar da kuzari da karfi ga namiji a lokacin da ya sha, amma illarsa shi ne: zai kasance idan har mutum ya saba da shansa, in har bai sha ba, ba zai iya tsinana komai ba. Na biyu kuma shi ne, zai takaita rayuwar jima’in mutum. Shi kuwa maganin Hausa dama dai babu wani bincike mai zurfi da aka yi a kai bare a gane adadin da za a sha da zai zama bai yi wa jiki yawa ba. Kuma za ta iya yiwuwa akwai wani adadi na guba a jikin ganye, saiwa ko sassaken maganin da ya kamata a ce an yi waje da shi kafin a sha mai amfanin, amma sai mu dirkawa cikinmu daga bisani wancan guba ya taru ya haifar da wata lalurar ta daban. Mafita…

Sau tari abin da ke sanyawa namiji ya gaza wani katabus na a zo a gani a yayin kwanciyar aure na da nasaba da irin abin da ya ke ci. Maza ya kamata ku fahimci cewa wadanan nau’ika na abinci na da tasiri wajen dakile mazantakarku kuma da zarar kun cire su daga jerin cimarku na yau da kullum, to fa ba sai kun sha wani maganin karfin maza ba, kuma matayenku za su yi murna da ku, kuma har lau babu wata fargaba ta samun matsalar lafiya sakamakon kokarin mutunta gida Ga nau’ikan abinci da za ka cire daga jerin abincinka ko kuma ka rage su matukar ragewa.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button