Labarai
Yanzu Yanzu: Saudiyya Za Ta Gille Kan mutane 5 Dake da Hannu a mutuwar Jamal Khashoggi
Advertisment
Biyo bayan kisan gilla da aka yiwa dan jaridan kasar Saudiyya, Jamal Khashoggi, an yankewa mutane biyar da ake zargi da hannu a kisan dan jaridan a kasar Istanbul, kasar Turkiyya.
Daily Mail ta ruwaito cewa dan sandan da ke gabatar da kara ya kuma sanar da tuhume-tuhumen da ake yi wa mutanen shida da ake zargi da hannu a kisan.
Legit.ng ta rahoto cewa dan sandan mai kara yace Saudiyya ta yarda cewa anyi wa Khashoggi wani allura na mutuwa a ofishin jakadancin kasar a ranar 2 ga watan Oktoba.
A baya mun ji cewa Kasar Saudia ta bayyana cewa zata biya diyyar dan jarida daya rasa ransa a lokacin da yake ziyartar ofishin jakadancin kasarsa a Turkiyya.
A yayin wata tattaunawa da CNN tayi da iyalan mamacin Salah da Abdallah sunce a dawo musu da gawar mahaifin su domin a binneshi a kasar sa wato Medina dake kasar Saudi Arabia, sannan sunce sun yadda da sarki Salman akan kokarin binciko wadanda sukayi wannan aika aika don a hukuntasu.
Wannan nuna rashin tausayi na kashe Kashoggi ya taba shugaban cin sarkin na Saudia.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com