Labarai

Allah Sarki Rayuwa: Amarya Ta Rasu Kwana 11 Bayan Aurenta

Wata amarya ta rigamu gidan gaskiya kwanaki kaɗan bayan tayi aure.

Angon amaryar mai suna Idris Elmustapha Daja, shine ya sanar da hakan a wani rubutu da ya wallafa dimokuraɗiya ta rahoto.

Allah Sarki Rayuwa: Amarya Ta Rasu Kwana 11 Bayan Aurenta
Allah Sarki Rayuwa: Amarya Ta Rasu Kwana 11 Bayan Aurenta

El-Mustapha Daja ya auri amaryarsa mai suna Maryam Muhammad Liman, a ranar 6 ga watan Janairun 2023, inda ta amaryar ta rigamu gidan gaskiya a ranar Laraba 18 ga watan Janairun 2023.

An yi jana’izar ta kamar yadda addinin musulunci ya tanada a gidan Hajiya Fatima Madugu, dakw akan hanyar Okada, cikin birnin Minna da safiyar ranar Laraba.

Sannan aka kai ta a makwancinta na gaskiya a maƙarbartar Gbakungu cikin birnin na Minna.

“Innalillahi Wainna Ilaihir Rajiun. Kwana sha ɗaya da aure, yau na rasa ta. Allah ya jiƙan ki da rahama ya sanya aljannah Firdausi ta zama makoma a gare ki.” Idris ya rubuta a Facebook.

Wani labarin : Amarya ta rasa Ido ɗaya ana tsaka bikinta sakamakon duka da ‘yan ƙato da gora suka mata

Wata Amarya mai suna Khadija Abdullahi ta makance a ido ɗaya sakamakon zabga mata gora da ‘yan ƙato da gora suka yi

Wannan ibtilain dai ya faru da Khadijah ne ana tsaka da shaglin bikin ta a unguwar Ɗantamashe da ke Kano.

A cewar Khadija Ƴan kungiyar sintiri na Vigilante na unguwar su ka yi mata wannan aika-aikan lokacin da suka zo raraka ana tsaka da kidan DJ

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button