Kannywood

Alhamdulillahi Darakta Ashiru Nagoma Ya Samu Lafiya Yayi Magana Zuwa Ga Yan Uwansa Yan Fim (bidiyo)

A yau ne Majiyarmu ta Hausaloaded ta samu labarin daga fitacciyar marubuciyar nan Fauziyya d suleiman da cewa darakta ashiru nagoma ya samu sauki yanzu haka yana gida wanda ta wallafa rubutu kamar haka.
“Alhamdulillah, cikin ikon Allah kamar yadda mu ka yi alkawarin karkashin foundation din mu @creativehelpingneddyfoundation za mu dauki nauyin kulawa da Ashiru Nagoma a asibitin Malam Aminu Kano, to cikin ikon Allah mun yi, yanzu haka asibitin sun sallame shi sai dai zai dinga zuwa ganin likita lokaci zuwa lokaci.
Akwai Wanda suka dinga kiranmu a wancan lokacin suna son taimaka masa mu ka ce su dan jira, to yanzu duk Wanda zai taimaka domin ganin ya ci gaba da samun kulawa zai iya tura taimakonsa ta account din da ya kasance na Dan’uwansa ne wato; 6323038066 Fedility bank, Abubakar Yusif Ibrahim.
Ga Wanda su ke son tuntubar Dan’uwansa kaitsaye za su Kira lambar wayarsa 08037247612
Real Fauziyya D. Sulaiman
Fauziyya D. Sulaiman Qforq”
Ga bidiyon da yake magana da bakinss zuwa ga yan uwansa yan Film da sauran al’umma.

[/video]

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button