Kannywood

Sharhin Fina Finai : Sharhin Fim Din “Tsammani”

Suna: Tsammani
Tsara Labari: Nazir Adam Salih
Kamfani: T.J Multipurpose Concept
Shiryawa: Sani Namu Duka
Bada Umarni: Falulu A Dorayi
Jarumai: Adam A Zango, Hadiza Aliyu Gabon, Fati Washa, Nuhu Abdullahi, Falalu A Dorayi, Yusuf Baban Chinedu, Lubabatu Madaki, Fati S.U, Lubabatu Madaki. Da sauran su.
Sharhi: Hamza Gambo Umar.
A farkon fim din an nuna Laure (Hadiza Gabon) a cikin gida tana ‘ko’karin wankewa ‘yarta Ikhram baki (Basma Baba Hasin) kafin daga bisani da suka dauki kayan sana’ar su na siyar da ‘kosai suka fita. Bayan Laure ta zauna a bakin wani kamfani inda take suyar ‘kosai sai Abbas (Nuhu Abdullahi) ‘kanin mai kamfanin yazo ya soma jan ta da rigima akan sai fa fada masa wanda ya bata ikon zama yin sana’a a gaban kamfanin su, Laure ta biye masa suka soma sa’insa har zuwa lokacin da mamallakin kamfanin wato Mudassir (Adam A Zango) ya iso wajen ya raba rigimar kuma ya bawa Laure ha’kuri sannan yaka ‘kanin sa Abbas suka shige ciki yana nuna mishi rashin dacewar wulakanta jama’a.

Yayin da a bangare daya kuma Mudassir yaje hira wajen budurwar shi Siyama (Fati Washa) sai ta dago hannuwa da nufin ta rungume shi, amma sai ya katse ta gami da nuna mata rashin dacewar hakan domin hakan ya sabawa addini da shari’a tunda basu riga sun yi aure ba kuma su ba muharraman juna bane, ganin hakan ne yasa Abbas ya fito daga cikin mota yana nunawa Mudassir takaicin sa bisa rashin goyon bayan da bai bawa Siyama sun rungumi juna ba, Mudassir bai biye masa ba suka tafi.

Da daddare Siyama tayi shirin fita zuwa club kamar yadda ta saba, amma sai mahaifiyar ta tayi ‘ko’karin dakatar da ita gami da nuna mata hakan da take yi ba daidai bane. Siyama bataji maganar ta ba ta fice ta tafi. Ita kuwa Laure bayan sun gama suyar ‘kosai sun nufo gida sai ‘yarta Ikhram take tambayar ta yaushe za’a mayar da ita makaranta? Laure ta rarrashe ta tare da nuna mata da zarar sun sami kudi zata mayar da ita makaranta.
Bayan Laure sun dawo gida sai ta tarar da Baba Chidu (Baban Chinedu)/mamallakin gidan da take haya yana zaune yana jiran ta don ya karbi kudin haya a hannun ta, amma sai ta nuna masa sam bata da kudin da zata basa, hakan yasa ya ‘kara mata gajeran lokaci gami da alwashin daukar mataki akanta idan bata biyashi kudin sa ba.

Laure ta shiga damuwa sosai saboda rashin kudin haya da zata biya ga ‘yarta tana yawan damun ta akan maganar komawa makaranta, hakan yasa ta hada ‘yan kudaden hannun ta taje don mayar da ‘yarta Ikhram makaranta, amma sai shugabar makarantar ta nuna sai an sakewa Ikhram sabon kayan makaranta sannan zasu karbe ta, bayan Laure ta dawo gida sai ta cigaba da sana’ar ta na siyar da ‘kosai, wanda anan suka hadu da masinjan Mudassir (Falalu A Dorayi) wanda sukan tsaya suyi hira aduk sanda yazo siyan ‘kosai wajen ta tasu tazo daya, kuma aduk lokacin da ya sayi ‘kosanta yakan tallata mata a wajen sauran ma’ailata wanda hakan yasa har me kamfanin wato Mudassir yakan sayi ‘kosai a wajen ta duk da ‘kanin sa Abbas yana takaicin hakan sosai.

Bayan dan wani lokaci Laure ta koma gida sai ta tarar Baba Chidu yazo da mota ya kwashe kayan ta daga cikin gida sannan kuma ya duba kayan a mota an tafi dasu ba’a bar mata komai ba sai kayan sawarta. Haka Laure da ‘yar ta suka dauki kayan su suka je wani gida me gidan ya kore su har zuwa sanda dare yayi musu a hanya inda suka hadu da Mudassir zai tafi gida ya dauke su don rage musu hanya amma sai ya fara biyawa ta gidan abinci suka ci abinci sannan ya mayar dasu ainahin gidan da suke wanda yake kulle da kwado, domin Laure bata fada masa halin da take ciki ba, bayan ya ajiye su ne ta dauki kayan ta ta tafi wajen masinjan Mudassir wanda yake gadi a gidan alhaji, a can ya bata wajen kwana amma sai Ikhram ta soma zazzabi sun fito neman magani ita da Megadi a hanyar dawowar su sai Abbas ya gansu ya soma zargin wani abu Laure da megadin gidan suke aikatawa hakan yasa ya Kore sa, yayin da ita kuma Laure suka hadu da Mudassir ya dauke su ya nemo wa ‘yarta magani sannan ya kawo ta gidan sa inda ta bashi labarin dalilin shigar su mugun hali a bisa mutuwar mijinta gami da ‘kuntatawar uwar miji wadda har asiri ta taba yi mata ta makantar da ita don kar a bata gadon mijin ta wanda a ‘karshe asalin hakan yasa Laure tabar garin kuma iyayen ta sun rasu shiyasa take yawo.

Jin hakan yasa Mudassir ya tausaya mata kuma yayi alkawarin taimaka mata, a ranar ne Siyama bydurwar Mudassir taga Laure a cikin gidan sa sai ta soma fushi gami da zargin ya fara neman matan banza, hakan yasa ko bayan Mudassir ya mayar da Laure gidan ‘yar uwar sa don ta zauna a can amma sai Siyama tazo wajen mahaifiyar sa ta nuna halayyar ta da Mudassir batazo daya ba don haka ta fasa auren sa. Jin hakan ne yasa ne yasa Mudassir ma yayi murna kuma ya kawo wa mahaifiyar sa Laure a matsayin wadda zai aura. A lokacin tuni Laure rayuwa ta soma yi mata kyau ta fita daga cikin ‘kuncin rayuwa.

Abubuwan Birgewa:

1- An nuna illar zaluntar dan Adam wanda daga ‘karshe alhaki yakan koma kan mai shi.
2- Jaruman sun yi ‘ko’kari wajen Isar da sa’ko Musamman Laure (Hadiza Gabon) tayi ‘ko’kari matu’ka.
3- Labarin ya tafi kaitsaye bai karye ba.

Kurakurai:

1- Lokacin da Abbas yazo wajen sana’ar ‘kosan Laure ya soma tambayar ta dalilin da tasa take musu suyar ‘kosai a gaban kamfani, tunda an nuna dama tana sana’ar a wajen shin me yasa Abbas bai taba tambayar ta dalilin zaman ta ba sai a wannan lokacin? Idan ana son nuna rashin goyon bayan sa akan sana’ar, to ya dace a nunawa me kallo cewa a wannan lokacin ta fara sana’a a wajen ba wai dama tana yi ba.
2- Lokacin da Baban Chinedu ya kori Laure daga gidan sa, me kallo yaga Laure taje gidan wata mace (Fati S.U) da nufin zata zauna a wajen ta. Shin wacce alaka ce tsakanin Laure da wannan matar? Tunda ance ‘yan uwan Laure basa gari ya dace a nunawa me kallo dangantakar dake tsakanin su wadda har tasa taje gidan ta kai tsaye don a bata wajen kwana.

3-Me kallo yaga lokacin da Mudansir ya dauko Laure a motar sa da jakar kayan su da nufin yakai su gida, amma sai aka gansu gaba daya a wajen sayar da abinci suna cin abinci suna hira. Shin Laure ce ta nuna masa tana jin yunwa da har yazo wajen siyar da abinci tare dasu? Tunda an nuna Laure da Mudassir a matsayin mutane masu mutunci da kamun kai bai dace su tafi wajen cin abinci tare ba, musamman tunda babu alaka mai karfi a tsakanin su, ya dace Mudassir ya wuce da ita gida kai tsaye in ma hirar su a Restaurant ta zama dole ko a mota ne sai suyi.

4- An nuna Laure da ‘yarta sun zo wajen me gadi don ya taimaka musu da wajen kwana, me kallo yaji me gadi yana yiwa Ikhram sannu duk da ba’a nuna cewar bata da lafiya ba. Amma a nunowa ta gaba sai aka nuna Ikhram jagab cikin zafin ciwo, shin dama me gadin yasan zatayi rashin lafiya ne da har ya fara yi mata sannu? Ya dace a fara nuna rashin lafiyar Ikhram din tun kafin megadin ya fara yi mata sannu.
5- An nuna ‘kawayen Siyama (Fati Washa) sun kawo ta gidan su cikin wani yanayi wanda bata san inda kanta yake ba, wanda dalilin hakan ne yasa Mudan ya tafi da ita gidan sa kafin ta dawo daidai, ya dace a nuna wa me kallo ainahin larurar da ta sameta.

6- Bayan Laure ta baro wajen megadin da ya bata wajen kwana tare da ‘yar ta wadda bata da lafiya, kwatsam sai aka ganta tare da Mudansir suna shawarar zai kaita gidan sa ta zauna, matsayin Mudansir na wanda yadau Laure a daren ya kaita gidan ta, ya dace ya nuna mamakin sa a lokacin da ya ganta tana gararanbar neman wajen kwana.

7- Sauti baya fita sosai a cikin wasu sina-sinan.
Karkarewa:
Fim din ya fadakar kuma labarin ya taba zuciya gami da rike me kallo, amma akwai abubuwan da ya dace su fi haka inganci. Wallahu a’alamu.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button