2019: Rikici Na Neman Barkewa Tsakankm Bafarawa Da Tambuwal Kan Wanda Za A Tsaida Takarar Gwamnan Sokoto A Karkashin PDP
Wani rahoto na cewa rikici ya fara bullowa tsakanin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal da tsohon gwamna Attahiru Dalhatu Bafarawa a kan wanda za’a tsayar takarar Gwamnan Sokoto.
Tambuwal dai na kokarin ganin an tsayar da tsohon Kwamishinan Ma’aikatar Lamurran Kananan Hukumomi ta jihar Hon. Manir Muhammad Dan-Iya ko tsohon Kwamishinan Kudi Alh. Sa’idu Umar, wanda da dadewa ake zargi Tambuwal na kokarin ganin ya gade sa, sai dai kusan canza shekar Gwamna Tambuwal sunan Sanata Ibrahim Danbaba Dambuwa ya fito a matsayin wanda ke son ya gade gwamnan.
A bangare guda kuma, ana zargin Gwamna Tambuwal da makarkashiyar ganin an canza Shugaban Jam’iyyar PDP na jihar Alh. Ibrahim Milgoma da yaronsa Alh. Mukhtar Maigona.
Milgoma wanda yake rike da mukamin shekaru 4 da suka gabata, babban na hannun daman Bafarawa ne a zamanin ANPP.
Daga Sakkwato Birnin Shehu