Ni da Aure Munyi Hannun Riga – cewar Adam a zango
Fitaccen jarumi kuma mawaki Adam A zango yayi wani rubutu da ya jawo cece kuce a kafar sada zumunta inda ya wallafa hoton wata yarinya yana mata addu’a Allah ya bata miji nagari.
Ga abin da yake cewa:
“Allah shi karbi aikin sayyada @hafsatu_2 #yar-aljannana! Ya baki miji na gari!”
Wannan rubutu ya dauki hankalin mutane suna ganin cewa ita ce wadda yake takon aure tunda baida mata a hanlin yanzu, bayan rabuwa da safiya yar birnin kebbi.
Shine mutane sunka dinga tufa albarkicin bakinsu.
Bayan nan sai jaurmin ya sake wallafa wani rubutu da ya baiwa mutane mamaki a kafar sada zumunta inda yake cewa.
“Allah yasa mu gama da duniya lafiya, mu mutu akan tafarkin muhammadu rasulullah (s.a.w)
“Ni ba miji nagari bane a gareta , shiyasa na mata addu’ar samun miji nagari wurin Allah.
Ni da Aure munyi hannun riga sai dai idan Allah ya ƙaddara wannan kuma babu yadda na iya.
“Fata nagari gareki Hafsat Allah ba sai taba baki mijin banza ba irina.
Bijahi Rasulullah “- Adam a zango