ZAN IYA YIN MAGANA LOKACIN PRE-KHUDBA ?
ZAN IYA YIN MAGANA LOKACIN PRE-KHUDBA ?
Tambaya
Asalamu Alaikum.
Allah ya karawa Dr Fikira da Fasaha.
Tambaya: idan mutum yazo masallacin jumaa ya samu ana pre-khudba shi kuma yana so ya karanta S Kahfi, to zai iya karantawa ya jiyar da kansa sautin karatun koda na kusa dashi suna ji?
Amsa
Wa alaikum assalam, zahirin hadisin da ya zo akan hana yin magana lokacin da ake hudubar juma’a bai game har da pre khudba ba,don haka za ka iya yin magana,ko ka karanta alqur’ani a lokacin da ake yinta.
Pre- khudba ta banbanta da huduba, saboda akan yi ta kafin Muktarin Juma’a ya shiga,sannan a lokuta da yawa za ka ga ba liman ne yake yi ba, Hani da umarni a shari’a abu ne da yake hanun Allah da manzonsa, wannan ya sa za’a takaita a inda ya zo a nan.
Hadisi mai lamba ta: 841 a sahihil Bukhari ya tabbatar da cewa : sai liman ya fito zai hau minbari ya fara huduba sannan mala’iku suke nannade takardun su,su zauna su saurari wa’azi da ambaton Allah, wannan sai ya nuna Pre-khudba ba ta daukar hukuncin hudubar juma’a wajan wajabta yin shiru da sauraro.
Allah ne mafi sani.
Dr Jamilu Zarewa. 3/Ramadan 1437