Labarai

Ta’asar Filato: Sojoji Sun Gabatar Da Wadanda A Ke Zargi

Rundunar tsaro na musammam ta “Operation Safe Haven’’ sun gabatar da mutum 3 da ake zargi da hannu a kashe kasha na baya baya nan data aukawa wasu sassan jihar Filato abin kuma daya tayar da hankullan jama’a a sassan kasar nan, an kama mutanen ne a yankin Gashish dake karamar hukumar Barkin Ladi na jihar ta Filato.

An gabatar da wadanda ake zargin ne a garin Jos tare da wasu mutum 14 dasu ma ake zarginsu da hannun a kisan da aka kashe fiye da mutum 86 wanda yawancinsu manoma ne ‘yan kauye ranar 24 ga watan Yuni.

An kama mutum 14 ne dangane da tashin hankali na baya baya nan ne, sai dai hukumomin sojoji basu bayar da sunayen wadanda aka Kaman ba.

Rikicin ya rutsa ne da kauyuka fiye 11 a karamar hukumar Barkin Ladi da kewaye inda bayan asarar rayuka dukiyoyi na miliyoin Naira suka salwanta.

Da yake gabatar da wadanda ake zargin, jami’in watsa labaran rundunar sojojin “STF”, Umar Adams, ya bayyana wa manema labarai cewa, an kamasu ne dauke da muggan makamai.Mista Adams ya ce, 2 daga cikin wadanda aka kama Fukani ne makiyaya yayin da 1 kuma dan kabilar Biram ne, kabilar da suka dade suna rikici da Fulani a kan wuraren kiwo da filayen noma. Kashe kashen Fulani makiyaya ya jefa harkar nomad a samar da abinci a yankin tsakiyar arewa cikin hakin kakanikayi.

Jihohin Binuwai da Taraba da kuma Nasarawa ne suka fi fuskantar rikice rikicen, kuma jihojin ne aka fi samun albarkatun gona a kasar nan.

Mista Adams ya kuma kara da cewa, an kama wadanda ake zargin ne a dai ai lokacin da suke kai hare haren. “Muna sane cewa, an kai hare hare a wasu kauyukan dake karamar hukumar Barkin, an kuma wadannan mutanen ne dangane da Karin da aka kai.“ A lokacin da jami’anmu ke fafutukar maharani ne aka kamasu da bindiga kirar AK47 guda 4 da kuma wasu bindigogi kirar gida guda daya”.

“Sauran mutum 14 kuma an kama su ne dangane da tashe tashe hankulan da aka samu ne a sassan jihar,”

Mista Adams, a halin yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike a kan wadanda ake zargin, ana kuma sa ran kara kama wasu mutanen a nan gaba.

Rahoto:-leadershipayau

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.comMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button