Shekau Ya Aike Da Kakkausan Gargadi Ga Sabbin Shugabannin Tsaro


Abubakar Shekau, shugaban tsagi guda na kungiyar Boko Haram ya fitar da sabon sautin murya inda ya yi magana game da nadin sabbin manyan hafsoshin Najeriya, inda ya ce babu wani abu da za su iya tabukawa da magabatansu ba su yi ba a yaki da ta’addanci a arewa maso gabas, jaridar HumAngle ta ruwaito.
A sautin da ya fitar mai tsawon mintuna tara da dakika 56, Shekau ya ce ya ji labarin yi wa tsaffin manyan hafsoshin tsaron murabus da maye gurbinsu da sabbi amma ya yi kira garesu su amshi musulunci.
A ranar Talata ne Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da yi wa tsaffin manyan hafsoshin tsaron murabus tare da maye gurbinsu da sabbi.
Kungiyoy da mutane da dama sun dade suna kira da shugaban kasar ya sauya manyan hafsoshin tsaron.
A cikin sabon sautin muryar da Shekau ya fitar, ya ambaci sunayen manyan hafsohin tsaron daya bayan daya da ayyukansu sannan ya yi kira garesu da su tuba domin babu wani abu da za su iya yi domin tarwatsa kungiyarsa.
“Leo Irabor, shugaban sojoji, ka tausayawa kanka, ka tuba ka amshi musulunci. Babu abinda zaka iya yi,” in ji Shekau.
Ya ce Manjo Janar Ibrahim Attahiru ya dena rudar kansa domin shi musulmi ne.
“Ko da kai musulmi ne amma kana yin shirka, yanzu kai ba musulmi bane,” in ji Shekau.
Wata majiya da ke da masaniya kan ayyukan Boko Haram ta shaidawa HumAngle cewa akwai yiwuwar kungiyar na shirya kai babban hari don ya zama ishara ga sabbin manyan hafsoshin tsaron cewa ba za su saduda ba.
Matsalar ta Boko Haram ta dade tana ci ma jami’an tsaron kasar tuwo a kwarya ganin har yanzu an kasa shawo kan matsalar.
Akwai dai fata mai yawa da ake akan wadannan sababbin shugabannin tsaron da Shugaba Muhammadu Buhari ya nada kan ganin an samu saisaituwar al’amura a bangaren tsaron kasar.