Labarai
Da Duminsa: Innalillahi wa inna ilaihi raji’un: Gawarwakin mutane 15 da ‘yan Bindiga suka kashe a Sokoto a daren Jiya
‘Yan Bindiga sun shiga garin Tara dake karamar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto inda suka ci karensu ba babbaka.
Sun kashe mutane 15 da jikkata wasu shida wanda yanzu haka suna Asibiti ana basu kulawa. Wanda suka rasu kuma an yi jana’izar su.
Wani mazaunin garin ya shaidawa Hutudole cewa lamarin yayi muni matuka kuma basu samu dauki daga wajan jami’an taaro ba.
“Wallahi na kasa tsayawa in ga gawarwakin saboda irin yanda suka wa mutanen mu” inji majiyar.
Allah yayi musu Rahama suka Allah ya tona musu asiri ya wargaza shirinsu idan masu shiryuwa ne Allah ya shiryesu