Kannywood

Sharhin Fim Din ” Fagen Baya”

09097438402 [email protected]
Suna: fagen baya
Tsara labari: A. U. Usman
Producer: Salihu Muhammad
Bada umarni: Nura Mustapha Waye
Kamfani: T.J multipopurse concept
Jarumai: Sadik Sani Sani, Maryam Jibrin Gidado, Bashir Nayaya, Rahma MK, Adam M Adam, Hajiya Zulai, Alhassan Kwalli, Baffancy, Mustapha B Maidala’ilu, Musa Mustapha da Ibrahim Soja.
Sharhi: Saddika Habib Abba
A farkon fim din an nuna yadda ake zaman lafiya tsakanin Saddam(Sadik S Sadik) tare da matarsa Islam(Maryam Gidado cikin kwanciyar hankali da kaunar juna ana cikin haka sai Islam ta fara rashin lafiya da suka je asibiti sai likita y tabbatar ai ciki ne da ita har na tsahon wata hudu da kwanaki, nan da nan labari yasha bam-bam Saddam ya tubure akan sharri likita ya yi wa matarsa domin su duka-duka watansu daya rak da aure a take ya dauketa suka tafi wani asibitin likita ta kuma aunawa aka tabbatar wa da Saddam abinda wancan asibitin na baya suka fada cikin tashin hankali Saddam da Islam suka dawo gida ya fara tuhumarta akan wanene ya yi mata ciki?
Islam ta tabbatar masa akan cewar cikinsa ne Saddam yaki aminta da hakan har ya dauketa ya maida ita gida Mahaifinta (Bashir Nayaya) tare da mahaifiyarta suka kafe akan cewar cikin Saddam ne domin ‘yarsu bata tsayawa da kowa sai shi, Saddam kuma fafur yaki amincewa da cewar cikinsa ne har mahaifin Saddam ya saka ‘yan sanda suka kama Saddam suka fara azabtarda shi akan lallai sai ya fadi laifinsa amma Saddam ya ki har sai da ta kai sun mika shi kotu sakamakon mahaifin Islam alkali ne sai ya tura su kotun abokinsa aka shiga aka fara shari’a Alkali ya tuhumi Saddam ya kara tabbatar da cewar shi bazai amshi cikin da bana sa ba, alkali ya dogara da wata hujja akan cewar Saddam ya taba daukar Islam ya kaita wani gida kafin suyi aure to anan ne ya yi wannan lalata da ita shi kuma Saddam ya aminta da cewar ya kaita gidan amma hira kawai suka yi babu abinda ya shiga tsakaninsu Alkali yaki aminta da abinda ya fada hakan tasa ya yankewa Saddam hukuncin zaman gida yari na shekara sha biyu tare da tarar naira dubu dari biyar abisa batawa Islam suna da ya yi da kuma rayuwarta dungurun gun, nan da nan aka tasa keyar Saddam gidan yari tun a wajen Islam ta fara nadama da tausayin Saddam hakan tasa har ta kai masa ziyara gidan yari tana bashi hakuri amma bai saurareta ba. ana cikin haka sai wani Barris.

Najib yazo abokin Saddam ne ya sami mahaifiyar Saddam ya shai da mata cewar lokacin da abun ya faru yana kasar waje amma tunda yanzu ya dawo baza su yarda ba za su daukaka kara mahaifiyar Saddam ta aminta da hakan Barri.Najib ya daukaka kara aka kai shari’ar kotun mahaifin Islam aka fara shari’a Alkali ya tuhumi Saddam akan har a lokacin yana kan bakansa? Saddam ya kuma cewa shifa bazai amsa laifin da ba nasa ba, Alkali ya fara tuhumar Islam a lokacin labari yasha bam-bam Islam ta tabbatarwa da Alkali shine ya yi mata wannan ciki hankali kowa a kotun ya tashi Alkali ya fara gumi.
Islam ta fara bada labarin baya ashe asali ma ita marainiyace mai shari’a ba mahaifinta bane kanin mahaifinta ne watarana yazo ya tarar da ita gidan babu kowa sai ita tun a lokacin ya fara haike mata bada son ranta bakuma duk sanda taki amincewa sai ya ringa tsoratar da ita tun a lokacin ciki ya bulla shine asalin samun cikinta amma Saddam ba shi da alaka wannan cikin kuma don kowa ya kuma gamsuwa Isla har ta nuna wani recording a wayarta a lokacin da mai shari’a yake aikata lalata da ita domin ya kara zama hujja nan da nan kotu ta hargitse shari’a kuma ta tashi Saddam ya fita daga zargi a idon duniya bayan sun dawo gida maishari’a ya fara jinya yana rashin lafiya har ya nemi yafiyar iyalinsa da Islam da Saddam duk suka yafe masa domin ko shari’arsu ta farko ma shine hada baki sukayi da wancan Akalin aka yankewa Saddam wancan hukuncin na zalunci, duk suka ce sun yafe masa shi kuma Saddam ya yi wa Islam alkawarin idan ta haihu zai maida ita dakinta domin har a lokacin yana sonta kuma abinda ya faru ba laifinta bane.

Abubuwan Birgewa:

1- Akwai darasi acikin fim din.
2- Labarin ya tafi har ya dire bai karye ba.

Kurakurai:

1- A farkon fim din yadda aka fara rubuto tsarin jerin sunayen ‘yan cikin fim din da sauran ma’aikatan fim din kwata-kwata ba dai-dai bane rubutun don wani abun ma bazai karantu ba.

2-Akwai lokacin da Saddam yazo gurin mahaifiyarsa yake fadamata cewar bazai iya cigaba da zama da Islam da ciki ba sai akaji mahaifiyar Saddam tana cewa ya yi hakuri ya cigaba da zama da ita shin mahaifiyar Saddam batasan dokar addini bane? kuma an nuna jaruman suna tafarkin addinin musuluncine domin a addinance auren mace da ciki haramun ne to ita mahaifiyar Saddam duk batasan wannan bane ko kuma wana hakurin take cewa Saddam ya yi tunda ita kanta ta tabbatar danta yana da gaskiya.

3-Bayan asiri ya tonu an gane cewar Mai shari’a shine ya yi wa Islam ciki amma masu kallo basu ga makomar shari’ar ba ko kuma don shi Alkali ne shikenan doka bazata hukuntashi ba idan ya yi laifi? yakamata ace an nunawa mai kallo yadda abubuwan suka kasance domin ya gamsu.

4- An nuno Saddam a wani office tare da wani mutumi suna muhawara akan shi bazai saka hannu a wata takarda ba domin shi ba macuci bane shin menene amfanin wannan hotan tunda bashida wata alaka da labarin fim din ko da shi ko babu shi labari zai tafi dai-dai hasali ma ba’a sake nuno makomar zancen ba.
5- ‘Ya’yan da aka nuna matar mai shari’a ta haifa a gaske kwata-kwata bazata haifesu ba sun yi girma.

6- wasu daga cikin jaruman fim din kwata-kwata basu dace ba kuma basu da kwarewa musamman lauyoyin fim din kwata-kwata basu nuna kwarewaba basu taka rawar data dace ba musamman lauyan daya ke kare Saddam a zamansu na kotun farko.
7- ko’a gida rikici ya faru irin na su Saddam da Islam idan za’a dai-dai ta abin za’ayi zama fiye da daya domin babban abu ne wanda yake bukatar bincike da nazari amma sai aka ga zaman da akayi a kotu na farko a shine aka gabatarda matsalar kuma akayi bincike kuma aka yanke hukunci duk a rana daya shin wacce irin kotu ce wannan kwata-kwata babu tsari acikinta.
8- An ga ‘yan sanda akan titi kawai sun sha gaban Saddam sun kama shi da bindigogi kamar wanda ya yi fashi kuma sunje sun garkameshi wannan abun babu tsari aciki kamata ya yi ace an je har gida an same shi idan ma tafiyar zasu yi dashi amma ba’a kan hanya yadda suka tareshi ba.

9- Lokacin da aka nuno Saddam da dansanda yana tuhumarsa a office ana jiyo sautin hayaniyar ma’aikatan fim din.
10- Kayan aikin fim din kamar camera da daukar hoto da abin daukar sauti ba wani fita suka yi yadda yakamata ba a fim din.
Karkarewa:
Labarin akwai darasi aciki amma akwai tarin kura-kurai wanda suka so su kashe labarin wanda da an lura dasu da fim din yafi haka kyau. Allahu a’alamu.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button