Nafison Auren Talaka Fiye Da Mai Kudi – Inji Maryam Gidado
Maryam Gidado tana daya daga cikin manyan jarumai mata a masana’antar fina-finan Hausa. Aminiya ta tattauna da ita kan harkar, inda jarumar ta tabo batutuwan da suka shafi harkar fim da kuma rayuwarta.
Ga yadda hirar ta kasance:
A Gabatarwa, wace ce Maryam Gidado?
Kamar yadda aka sani, sunana Maryam Jibril Gidado, wacce aka fi sani da ‘Maryam Babban Yaro.’
Na samu wannan suna ne tun daga lokacin da muka yi fim da Adam A. Zango mai suna ‘Babban Yaro.’ An haife ni a watan Disamba a 1988 a garin Jos. Na fara makaranta a Hassan Memorial, sai aka mayar da ni firamare ta LGA Gangare, sannan na yi makarantar Arabiyya ta Sakandire a Bauchi Road, duka a Jos.
Sannan na je na yi Diploma a bangaren kwamfuta a wata makaranta daban. Daga nan na koma Bauchi na nemi in yi HND, amma ban samu ba sai na yi diploma a bangaren kididdiga. Sai kuma na ci gaba har na yi HND a nan, sai na dawo Jos na yi digirina a Jami’ar Jos.
Ko Maryam ta taba yin aure?
To yanzu idan na ce ma ban taba yin aure ba sai a yi mini dariya a matsayina na Bafulatana, kasancewar kowa dai ya san ka’idar Fulanin daji yi wa ’ya’yansu aure da wuri. Bayan na gama jarrabawar WAEC da NECO aka yi mini aure.
Ina shekara sha hudu na haifi ’yata ta farko, bayan shekara daya da auren ke nan. Don haka shekara goma sha hudu na ba ’yata ta fari. Yanzu ka ga ta shiga shekara sha daya ke nan.
To yaya aka yi kika samu kanki a harkar fim?
Ni dai gaskiya da ina kallon fim ne kawai, amma ina tunanin shirme ne kawai, domin idan na ga ’yan fim har zaginsu nake yi don ban taba tunanin zan yi fim ba.
Daga baya sai na ga yadda abin yake fadakarwa. Na ga wasu ma sun Musulunta ta hanyar fim. Sai na ga abin wa’azi ne.
To, a baya kin fada mana yadda aka yi miki aure har kika haihu. Sai dai ba ki fada mana ko kun rabu da mijin ko mutuwa ya yi ko kuma da aurenki kike yin fim ba?
To, a gaskiya ba zan iya fada ba. Saboda a duniya babu abin da ya kai sirri dadi. Idan ka rufa wa wani asiri Allah Zai rufa naka. Kuma tsakanin mata da miji sai Allah. Don haka wannan mutane su yi hakuri.
Shin wannan dan naki na biyu babansu daya da ’yarki ta farko?
Ba daya ba ne. Bayan mun rabu da mijina na yi wani sabon aure. Lokacin da na auri mahaifin dana ma har na fara harkar fim. Ina da cikinsa ya gudu ya bar ni har na haife shi yanzu shekarun dana na biyu bakwai ke nan.
Abin nufi a nan shi ne, kun rabu da shi ne ko rasuwa ya yi?
To, in dai wannan ne ba rasuwa ya yi ba, yana nan da ransa, sannan ina da cikin dana na biyu wata daya ya tafi ya bar ni, har zuwa yanzu mahaifinsa bai zo wajen da yake ba. Sai dai ya turo a dauki hotonsa, kuma zai iya kira ta waya su yi magana, amma dai yana nan a Kaduna kawai dai tafiyar da ya yi ya bar ni don wani dalili ne na daban.
To daga nan sai me ya biyo baya?
Kai dai a bar maganar haka, don sirri yana da dadi.
Ki fada mana yadda aka yi kika samu kanki a harkar fim da kuma shekarar da kika fara?
A gaskiya na manta shekarar da na shigo, amma dai na fara ne da albam din Mahmud Nagudu mai wakar ‘Garin So Nisa’ amma fim din da aka fara yi mini shi ne wani fim mai suna ‘Ragowar Yaki,’ lokacin da muke yi a Jos da ni da Ali Nuhu.
Shi ne fim dina na farko da na fara yi a duniya, kuma da ma tun da na fara fim ban fara da mai tallafa wa jaruma ba, da jaruma na fara. Kodayake da farko mutane sun dauka albam nake yi ba fim ba, saboda shi ne na fara. Sai daga baya na zo na shiga fim din su Alma, inda na yi ‘Ragaya’ da ‘bingyal da ‘Mukaddari’ da sauransu.
Ko za ki iya bayyana yawan fina-finan da kika yi?
Gaskiya ba zan iya fadar adadinsu ba. Don ka ga a wata zan iya yin fim biyu ko uku, to yaya zan iya sanin fim din da na yi a tsawon lokacin da na yi a harkar fim? Sai dai zan iya fadar wasu kadan daga cikinsu, musamman wadanda ba su dade ba kamar ‘Babban Yaro’ da ‘Wata Hudu’ da ‘Munafikin Mata’ da ‘Al’ajabi’ da ‘Zawarawa’ da ‘Fulani’ da ‘Sultan’ da ‘Basaja.’ Ina ji da su a cikin fina-finaina.
Akwai lokacin da kika yi wani tashe sai kuma aka daina ganin ki a harkar fim. Hakan ya sa ake cewa ko kin yi aure