Labari Mai Dadi : Gwamnatin tarayya ta fadi lokacin da zata fara biyan sabon tsarin albashi
Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ta sanar da zuwa karshen watan Satumba na wannan shekarar a matsayin lokacin da za ta fara biyan sabon tsarin albashi ga ma’aikatan ta a dukkan fadin kasar nan.
Wannan dai kamar yadda muka samu na kunshe ne a cikin bayanin maraba da babban ministan kwadago da samar da aikin yi na kasar Sanata Chris Ngige ya yi jiya Litinin lokacin da yake jawabi a lokacin bikin cikar kungiyar kwadago ta kasa shekara arba’in da kafuwa.
Ministan ya bayyana cewa tuni har shire-shiren tabbatar da sabon tsarin albashin yayi nisa saboda a cewar sa, wannan gwamnatin da kuma shugaba Buhari suna da matukar tausayin ma’aikatan kasar.
A wani labarin kuma, Fadar shugaban kasar Najeriya dake a unguwar Villa, babban birnin tarayya Abuja ta bayyana a jiya cewa su fa su shugaba Buhari da mataimakin sa Yemi Osinbajo batun zarcewa bisa mulki a zaben 2019 ma bai dame su ba.
A maimakon hakan, kamar yadda muka samu daga fadar, an bayyana cewa su shugabannin kawo yanzu ba abun da ke a ran su irin tabbatar da samun cigaba mai dorewa a kasar tare kuma da jin dadin ‘yan Najeriya.

![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)






