Makarantar Dahiru Usman Bauchi Ta Yaye Mahaddatan Alkur’ani Mutum 898
Kimanin dalibai 898 ne a halin yanzu suka kammala haddar Al-Kur’ani mai girma a makarantun babban shehin malamin addinin Islamar nan kuma jagoran marhabar Darikar Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Usman Buchi sannan kuma wasu 312 sauke ba ta hanyar handaccewa ba a fadin kasar nan.
Darakta Janar din dake kula da harkokin ilimi a wata Gidauniyar ta Shehin malamin dake kuma zaman da ga Malamin mai suna Sheikh Sidi Aliyu Sise Dahiru Usman Bauchi da kuma Malam Hassan Adam ne suka bayyana hakan a yayin jawaban su daban daban lokacin da ake yaye wasu daliban a jihar Bauchi.
NAIJ.com dai ta samu cewa Sheikh Sidi Aliyu Sise ya ce wannan adadin na daliban sun fito ne daga wasu makarantun dake a rassa daban-daban a jihohin Kebbi, Bauchi, Kano, Kwara, Kaduna , Adamawa, Sokoto, Zamfara,Gombe da kuma jihar Neja. Mai karatu dai zai iya tuna cewa a kwanan baya mun ruwaito maku cewa Shehin malamin yana wata rashin lafiya inda kuma aka nemi jama’ar musulmi da su taimaka masa da addu’o’i.


![[Bidiyo] Dalibin Sheikh Bello Yabo Ya Mayarwa Malam Murtala Bello Sokoto Martani](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2022/08/Bello-Yabo-vs-Murtala-Bello-Sokoto-.jpg?resize=390%2C220&ssl=1)

