Sababbin Jarumai Guda (5) Da Ke Haskakawa A Masana’antar kannywood
Tauraron su na haskawa kuma da alama sun shirya damawa da sauran fitattun jarumai dake masana’antar
Sunayen sabbin jarumai 5 dake tashe a dandalin kannywood a halin yanzu ciki har da shaharraren mawakin hausa.
Tauraron su na haskawa kuma da alama sun shirya damawa da sauran fitattun jarumai dake masana’antar.
Ga jarumai kamar haka:
1. Rashida Lobbo
Tana cikin jarumai da suka amshi kyauta a bikin karrama jarumai da mujallar city people ta shirya a jihar Legas cikin wannan shekara
2. Maryam Yahaya
Tun fitowar ta a cikin shirin “Mansoor” wannan jarumar ta samu karbuwa a farfajiyar kannywood domin bayan fitowar a shirin ta samu damar fitowa a fina-finai da dama.
Matashiyar wanda ta shigo farfajiyar yin fim da kafar dama ta shaida wa BBChausa cewa Ba harkar fim kadai ke gabanta. Latsa nan domin karanta dalilin
3. Umar M.shereef
Shima wannan mawakin ya garzayo farfajiyan yin fim kuma tun bayan fitowar sa a “Mansoor” masu shirya fina-finai na Kannywood sun kara bashi damar fitowa fina-finai daban daban.
Zai kara haskawa a cikin watni sabon fim mai suna “Mariya” tare da abokiyar aikin sa na cikin shirin “mansoor” watau Maryam yahaya.
4. Amal Umar
Wannan matashiya ta haska a fina-finai daban daban kana tana damawa da jiga-jigan gwarzayen masana’antar
5. Garzali Miko
Babu shakka wannan matashin jarumi ya shirya bayyanar da basirar shi na yin fim kuma da alamu direktoci sun gani a jikin shi.