Sports

SPORT:RADE-RADIN SAYAN YAN WASA- LAHADI 23/7/2017

RADE-RADIN SAYAN YAN WASA- LAHADI 23/7/2017 

1. Manchester City ta kammala sayan dan wasan bayan Real Madrid Danilo mai shekaru 26 akan kudi £26.5m. 

2. Koci Ernesto Ververde ya jaddada kudirinsa na ci gaba da rike Neymar a Barcelona bayan da dan wasan ya ci kwallaye biyu a wasan sa da zumunta da suka doke Juventus 1-2. An rawaito cewa PSG ta shirya biyan £199m akan dan shekaru 25 din, amma shigaban Barca Josep Maria Bertomeu ya fadawa sashin wasanni na BBC cewa dan kasar Brazil din ba na sayarwa bane. 

3. Mai tsaron raga David De Gea zai ci gaba da zama a Manchester United kashi dari-bisa-dari inji koci Jose Mourinho. Ana alakanta dan shekaru 26n da komawa Real Madrid. 

4. Manchester City da amince da cinikin £52m na sayan dan wasan bayan Monaco Benjamin Mendy mai shekaru 23. 

5. Dan wasan bayan Manchester City Aleksandar Kolarov mai shekaru 31 ya koma kulob din Roma akan 4.3m. 

6. Barcelona ta shirya kai tayin £80m ga Liverpool akan dan wasan tsakiyar kasar Brazil Philippe Coutinho mai shekaru 25. 

7. Kocin Liverpool Jorgen Klopp ya ce Coutinho na jin dadin zama a kulob din bayan da ya tattauna dashi bisa sha’awar da Barcelona ta nuna akansa. 

8. Barcelona ta amince cewa sayan Coutinho zai taimaka wajen ci gaban zaman Neymar a kulob din, tunda kasarsu daya. 

9. Arsene Wenger ya karyata maganar cewa dan wasan gaba Alexis Sanchez mai shekaru 28 na gab da komawa PSG akan £70m. 

10. Har yanzu Liverpool da Man. City na rige-rigen sayan dan wasan gaban Monaco Kylian Mbappe mai shekaru 18. 

11. Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya amince cewa dan wasan gaba Cristiano Ronaldo zai ci gaba da zama a kulob din, bayan da rahotanni suka bayyana cewa yana son barin kungiyar bisa zarginsa da kin biyan haraji a kasar ta Sifaniya. 

12. Chelsea za ta kai tayin neman sayan dan wasan tsakiyar Arsenal Alex Oxlade-Chamberlain nan da awanni 48, amma za ta fuskanci takara daga Manchester City akan dan shekaru 23n. 

13. Manchester United na son sayan dan wasan tsakiyar Chelsea Nemanja Matic mai shekaru 28, bayan da suka kasa sayan dan wasa Tottenham Eric Dier mai shekaru 23. 

14. Tayin £60m da United ta kai na neman dan wasan tsakiyar PSG Marco Verratti mai shekaru 24 na cikin kila-wa-kala, saboda kulob din na Faransa na so a bashi dan wasan gaba Anthony Martial mai shekaru 21 a cinikin. 

15. Dan gaban Barcelona Lionel Messi mai shekaru 30 ya fadawa kulob din cewa su sayo dan gaban Juventus Paulo Dybala mai shekaru 23. 

16. Dan kasar Algeria Mahrez zai iya watsi da tayin komawa Roma, a kokarinsa na tilasta cinikin £35m don ya koma Arsenal. 

17. An yiwa Arsenal tayin sayan dan wasan tsakiya Rafinha mai shekaru 24 daga Barcelona.

#Admin

#AnasGarbaBaba

YI SHARHI, GYARA KO TAMBAYA.

Ku kasance da ®www.hausaloaded.com

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA