sport:- Mancherster United ‘za ta nemi Mesut Ozil’
Rahotanni a Ingila na cewa kungiyar kwallon kafa ta Manchester United za ta nemi dan wasan Jamus Mesut Ozil a watan Janairu.
Labarin da jaridar the Independent ta wallafa yana zuwa ne a daidai lokacin da ake kwan-gaba-kwan-baya kan sabuwar yarjejeniya tsakanin dan wasan da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal.
Mesut Ozil ya koma Arsenal ne daga Real Madrid kan kudi fam miliyan 42.4 a shekarar 2013.
Yana daga cikin manyan ‘yan wasan kungiyar da sukan sha suka a duk lokacin da ba ta yi katabus ba.
Sai dai ya sha nanata irin rawa da kuma kokarin da shi da sauran ‘yan wasan kulob ke takawa a duk lokaicn da aka bujuro da irin wannan zargi.
bbchausa
Join Our WhatsApp Channel
Get verified job vacancies, career tips, scholarships and opportunities delivered straight to your phone, free and as soon as they're posted.


